Nijar: Yan majalisar dokoki na rikon kwarya
May 2, 2025'Yan majalisar za su kasance mashawarta ga majalisar ceton kasa ta sojoji ta CNSP da kuma gwamnati kan batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, zamantakewa da kuma al'adu. Tuni dai ‘yan kasar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan aikin da ke a gaban majalisar rikon da kuma abin da suke jira daga gare ta. .
A karkashin wani kudirin doka da ya sanya wa hannu a ranar daya ga watan Mayun 2025, shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tiani, ya nada mambobin Majalisar dokokin rikon kwaryar Conseil Consultatif de la Refondation wato CCR a takaice.
Majalisar rikon ta kunshi wakilai 189 maza da mata daga yankuna takwas na kasar Nijar da suka hada da sojoji da farar hula da sarakunan gargajiya da malaman addinai da mata ‘yan fafutika, da matasa da ‘yan farar hula da dai sauran rukunnan al'umma daban-dabam na kasar.
A nan gaba ne dai za a kaddamar da zaman majalisar rikon kwaryar mulkin sojan kasar inda a zamanta na farko za ta zabi mambobin kwamitin gudanarwa da zai yi aiki a tsawon wa'adin shekaru biyar da majalisar za ta yi. Majalisar da a ko da yaushe shugaban kasa na iya rusa ta idan ya ga ba ta aikin kirki domin maye gurbin mambobinta da sabbi.