Nijar ta tsaurara yadda Turawa ke samun visar kasar
August 27, 2025A cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 20 ga Agusta wacce kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya tabbatar a ranar Talata, ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya koka cewa ‘yan Nijar "har yanzu sai sun je kasashe makwabta domin kammala aikin neman visar zuwaTurai.” Ya bayyana cewa Nijar ta roki hukumomin Turai da ke Yamai da su rika bayar da visa a nan, amma har yanzu ba a kula su ba.
Daga yanzu, ofisoshin jakadancin Nijar da ke Geneva, Ankara da Moscow ne kawai ke da ikon bayar da visa ga ‘yan kasashen Italiya, Netherlands, Jamus, Belgium da kuma Birtaniya,” in ji ministan. Amma ministan ya ce masu rike da fasfo na diflomasiyya ko na hidima za su iya samun visa a ofishin jakadancin Nijar da ke Brussels, a cewar ministan.