NIjar ta sallami Saadi Gadhafi
September 7, 2012Talla
Nick Kaufman ya fada wa kamfanin dillacin labaru na Associated Press cewar ya samu wata wasika daga ministan harkokin wajen Nijar wanda a ciki ya ce zai amince da barin Saadi kasar muddin wata kasa dabam za ta karbe shi. Kaufman ya yi madallah da wannan mataki. A wancan shekara ne Saadi ya arce zuwa Nijar bayan faduwar gwammatin mahaifinsa. Tun daga wannan lokaci ne kuma ake rike da shi a cikin wani yanayi da lauyar ya kira daurin talala. Shi dai Saadi Majalisar Dinkin Duniya ta dora masa haramcin yin tafiye tafiye. To amma babu wani sammace da kotun hukunta miyagun laifuka ta kasa da kasa ta bayar a kansa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi