Nijar ta faɗa a ricikin siyasa
April 3, 2012
A jamhuriyar Nijar ƙawancen jamiyyun adawan ƙasar a karkashin
jagorancin jamiyyar MNSD nasara, sun fitar da wata sanarwa a birnin Yamai inda su ka bayyan matsayinsu akan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na tsige wasu ministoci guda ukku da aka jima ana cecekuce akansu a kasar. Haka zalika jamiyyun adawan sun bayyana fargabarsu a game da yiwuwar yaɗuwar rikicin ƙasar Mali zuwa cikin kasar ta Nijar da kuma akan matsayin kungiyar ECOWAS a cikin wannan rikici na kasar Mali.
Hujjar gwamnati
Ko da ya ke gwamnatin kasar Nijar ba ta fito ta yi bayani ba dangane da dalillanta na tsige ministocin nata guda ukku da ta yi a jiya yan Nijar da dama dai na danganta matakin tsige ministan kudi da na ma'aikatar gine-gine da batun kama su da kotun tsarin milki ta yi da laifin taka kundin tsarin milkin kasar ta hanyar bayar da kwangila ga wani dan majalisar dokoki a yayin da ita kuma ministan ma'aikatar sufuri ta kasa ake danganta matakin korar tata da laifin kamata da aka yi da hannu dumudumu a cikin batun wani pasakwarin goro a kasar Saudiyya a lokacin aikin hajjin da ya gabata.
Maye gurbin ministoci
Tuni kuma gwamnatin ta maye gurbinsu da wasu sabbin ministoci, inda aka nada Malam Jule Baye a ma'aikatar kudi sai kuma Ibrahim Yakuba a ma'aikata gine-gine. To amma da ya ke tsokaci dangane da wannan mataki da gwamnatin ta dauka, kawancan jamiyyun adawar kasar Nijar wanda ya jima yana tayar da jijiyoyin wuya akan yanda shugaban kasa ya ki daukar wannan mataki a baya ta bakin sakataran yada labaran jamiyyar MNSD nasara malam Isuhu Tambura, ya koka bisa mataki n da gwamnati ta ɗauka
Rikicin Mali
A wani gefen kuma a cikin sanarwar da ta fitar kawancan jamiyyun adawar ya bayyana fargaba a game da yiwuwar yaduwar rikicin tawayen da ake fuskanta a kasar Mali zuwa cikin kasar Nijar. Dangane da wannan rikici na kasar ta Mali dai a cikin sanarwar tasu kawancan jamiyyun adawan kasar ta Nijar sun kuma bayyan matukar mammakinsu dangane da yadda suka ce kungiyar ECOWAS ta ke tunkarar lmarin na ƙasar Mali.
Wani abun lura dai a nan shine ga bisa dukkan alamu matakin tsige ministoci ukku da gwamnati ta yi, bai sanya an rabu da bukar ba a tsakninsu da yan adawa, wadanda yan majalisarsu suka bada takardar neman tsige gwamnatin baki daya a gaban majalissar dokokin kasa a yayin da kuma a gefe daya rikicin kasar MALI ke neman bude wani
sabon babi na sa insa tsakanin bangaran masu mulki da yan adwan kasar ta Njar.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman