Malam Mamman Barka ya rasu yana da shekaru 62
November 21, 2018Talla
Mamman Barka na daya daga cikin wadanda suka yi fice tare da fitar da sunan Nijar a kasashen ketare, ta hanyar wakokin gargajiya hadi dana zamani a ma'udu'ai daban-daban da ke fadakar da al'umma musanman matasa.
An haifi mawakin shekaru sittin da biyu da suka gabata a garin Tasker na yankin Zinder a Arewa maso Gabashin kasar. A shekarar 2002 tare da tallafin hukumar UNESCO mawakin ya kaddamar da bincike kan wani nau'in kayan kida na Biram da ake bugawa a yankunan kasashen Tafkin Chadi.
Barkayi kamar yadda aka yi wa mawakin lakabi, ya sha cin kyaututuka, ya kuma sha wakiltar kasar a kasashen waje ciki har da Kasar Jamus don gabatar da wakokinsa. Maman Barka ya rasu ya bar mata guda da 'ya'ya goma.