Nijar: Sabuwar yarjejeniyar hakar ma'adanai
April 4, 2025Hakar ma'adanai a yankin Sahara na Agadez na Jamhuriyar Nijar da aka bai wa kamfanonin cikin gida lasisi abu ne da ake fata ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Amma ko manufa ce da ake ganin za ta haifar da abin da ake bukata? ganin duk gwamnatocin mulkin soja a kasashen Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar suna kara duba hanyar bunkasa kamfanonin cikin gida.
Ulf Laessing na Gidauniyar Kanrad Adenauer ta Jamus wanda yake jagorancin yankin Sahel ga abin da yake gani kan matakin:
"Nijar ta bayyana fara hakar ma'adinin Copper daga yankin arewacin kasar da taimakon kamfanonin cikin gida. Wannan shi ne manufar daina dogaro da kamfanonin kasashen ketere, haka batun yake kan makamashin Uranium. Yaya nasarar hakan, wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Ma'adanan na arewacin kasar kusa suke da kasar Libiya, inda ake fuskantar matsalolin tsaro kana talauci ya yi katutu. Wannan matakin gwamnatin ya yi kama da abin da ake gani a kasahsen Burkina Faso da Mali na dogara da cikin gida maimakon kasashen Yamma, amma wannan ba manufa ce da za ta yi nasara ba."
Wannan hakar ma'adanan gagarumin aiki ne na fitar da kusan ton-dubu-uku duk shekara. Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar tana fata haka zai kirkiri ayyuka ga daruruwan matasa. Sannan matakin zai samar da kudin shiga ga gwamnati. An shafe shekaru gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana hakar ma'adanin Uranium a wannan yanki. Amma tun da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchian suka kwace madafun ikon kasar ta Jamhuriyar Nijar a watan Yulin shekara ta 2023 hakar ma'adanin Uranium ya tsaya. Kuma gwamnatin ta samu sabani da kasar Jamhuriyar Benin mai makwabtaka, inda ake bi wajen fitar da kayayyakin Jamhuriyar Nijar zuwa kasashen duniya.
Duk gwamnatocin kasashen da aka yi juyin mulkin suna kara nesanta da kasashen Yamma. Seidik Abba dan jarida masani harkokin rayuwa ya ce haka na da nasaba da tarihi:
"An dade da burin ganin fadada kasashen da ake dangantaka da su. Ko bayan kawo karshen mulkin mallaka, huldar tattalin arziki da kasashen Yamma ke mamaye komai. Karkashin tsarin kasashen Yamma ke da ta cewa, inda ga misali su ne ke saka kudin kayayyaki da suke saya daga kasashen Afirka. Wannan abu ne da ake gani na rashin adalci a Afirka."
Gwamnatin mulkin sojan ta Jamhuriyar Nijar ta daina mutunta alkawuran da tsohon Shugaba Mohamed Bazoum ya saka hannu a kai gabanin kifar da shi. Kasashen na Mali da Jamhuriyar Nijar gami da Burkina Faso suna da ma'adanai masu tasiri da suka hada da Uranium, da Goran-ruwa da zinare gami da man fetur.