Nijar: Sabon takun saka da kamfanonin mai na China
March 14, 2025Gwamnatin Nijar din na zargin kamfanonin da kin mutunta dokokin aiki a kasar da ma na yarjejeniyar aiki da suka sanya wa hannu. Sai dai a yayin da wasu ‘yan Nijar ke yaba wa da matakin wasu na ganinsa a matsayin barazana ga makomar huldar Nijar da China da ma tattalin arzikin Nijar din baki daya.
Ko da shi ke cewa a hakumance gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan mataki ba, amma wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin sun tabbatar da cewa tun a ranar Larabar da ta gabata Shugaban kasa Janar Abdourahmane Tchiani ya bayar da wa'adin sa'oi 48 ga manyan daraktacin kamfanonin CNPC mai aikin hakar man fetur a Nijar da na kamfanin WAPCO da ke kula da jigilar danyen man Nijar ta bututu zuwa tashar ruwan Cotonou da kuma na Babbar matatar mai ta SORAZ su bar kasar baki daya.
Majiyoyi na cewa hukumomin kasar ta Nijar na zargin kamfanonin kasar Chinar da aikata laifuka dabam-daban da suka hada da kin mutunta yarjejniyar horas da ma'aikata ‘yan Nijar, da ci da gumin ma'aikatan Nijar ta hanyar basu albashin da bai taka kara ya karya ba a gaban takwarorinsu na Chinar da ma shirya makarkashiyar da ta haddasa matsalar karancin man fetur a baya bayan nan a kasar. Malama Falmata Taya ta kungiyar M62 ta ce matakin korar ‘yan China hannunka mai sanda ne ga sauran kamfanonin ketare masu aiki a Nijar.
Shi ma Alhaji Baba Almakkiya na kungiyar SEDEL/DH- Niger goyon baya ya kawo ga matakin korar ‘yan China. To amma Malam Tchanga Tchalimbo cewa ya yi matakin korar yan Chinar bai basu mamaki ba. Shi ko Malam Ghaliou Alhassane danganta matakin ya yi da bashin kudi miliyan dubu 240 da Nijar ta ciwo daga kasar China a 2024
Yanzu haka dai ko baya ga korar wadannan manyan daraktoci na kasar China, gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kuma sanar da kwace lasisin aiki na babban Hotel na SOLUXE mallakar China da ke birnin Yamai, yayin da a share daya Janar mai bulala ya ba da izinin rufe asusun ajiyar kudi na babbar matatar mai ta kasa ta SORAZ. Kawo yanzu dai kasar ta China ba ce uffan ba. Kuma ‘yan Nijar sun zura ido su ga yadda za ta kaya tsakanin gwamnatin da kasar ta China wacce ke aikin Uranium da Man fetur da kuma gine-gine a kasar ta Nijar musamman tun bayan juyin mulki.