Nijar: Nazari kan bitar kasafin kudin 2025
May 30, 2025Sama da shekaru 10 kenan, kowace shekara kungiyar Alternative ke shirya bitar kasafin kudin kasa na shekara a wani mataki na sa ido don ganin ko gwamnati na mutunta tanadin dokar kasa game da yadda ya kamata ta aiwatar da kasafin kudin yadda zai yi daidai da muradun al'ummar kasa.
Mutane sama da 120 ne da suka hada da shugabannin kungiyoyin farar hula da na makiyaya da manoma da malaman makaranta da na kiwon lafiya da masana ilimin tattalin arziki da tsoffin 'yan majalisar dokoki da sauran rukunnan al'umma daga yankuna takwas na kasar ta Nijar suke halartar wannan taro inda a tsawon kwanaki uku za su yi fidar kasafin kudin na shekarar 2025 domin sanin yadda gwamnatin ta kasafa kudin tsakanin fannonin rayuwar kasa da na al'umma.
Ita ko Malama Kare Malam Ibrahim da ke halartar taron daga Jihar Diffa nuna damuwarta ta yi dangane da yadda ta ce kasafin kudin ya fi ware kaso mai tsoka ga ma'aikatan gwamnati
To amma mahalarta taron bitar sun yaba da irin ci gaban da Nijar ta samu a fannin kudaden da za su shigo mata ta hanyar arzikin ma'adanai. Malam Aissami Tchiroma masanin dokokin hakar ma'adanai wanda ya gabatar da makala kan wannan maudu'i a taron bitar
Wakilan kungiyoyin farar hula da ke halartar taron daga yankunan takwas na kasar sun yaba da wannan tsari da kungiyar Alternative ta bijiro da shi na binciken kasafin kudin kasa.
Za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da wannan taro inda daga karshe mahalartan za su fitar da jerin shwawari ga gwamnati na irin gyare-gyaren da ya kamata ta kawo ga kasasfin kudin kasar yadda zai fi amfanin al'ummar kasar