Nijar na samun ci gaba mai ban mamaki
February 26, 2025Ministan kula da harkokin man fetur Dr. Sahabi Oumarou ya bayyana rawar da man fetur ke takawa wajen juriyar tattalin arzikin kasar Nijar bayan abubuwan da suka faru a watan Yulin 2023, da kuma tasirinsa wajen kulla yarjejeniyoyi kan harkokin mai da iskar gas da kasashe da dama na Afirka. Ministan ya kuma sanar da bincike da suke aiwatarwa a matatar mai ta Damagaram da kuma halin da ake ciki yanzu baya shekaru kimanin 14 da soma aikin wannan matata.
Sai dai a fuskar kungiyoyin fararan hula masu sa ido kan ma'adinan karkashin kasa, ta bakin Aissami Tchiroma, an samu babban ci gaba a fannin bada haske kan arzikin kasa:
A Fannin samar da ayyukan yi, nan ma za a iya cewa bangaren na man fetur ya taimaka wajen samar da guraben aikin yi inda ‘yan Nijar 409 suke aiki a kamfanin CNPC yayin da wasu 442 ke aiki a matatar mai ta SORAZ sai kuma wasu 85 da suke cikin kamfanin WAPPCO mai kula da bututun mai da aka shimfida daga Nijar zuwa tashar ruwan Cotonou a kasar Benin, baya ga sauran ayyukan yi da ba na kai tsaye ba, da mutane da dama ke samu ta hanyar kwangila. Kuma a cewar Issoufou Kado Magaji masanin tattalin arziki kuma tsohon ma‘aikacin baitulmalin kasa, idan aka dauki kwararan matakai na sa ido dole yan kasa su samu walwala:
A Nijar dai kowane Minista na da aiki takamaimai da shugaban kasa ya damka a hannunsa da shi ne zai mayar da hankali da bada mahimmanci kuma ofishin ministan mai an damka masa bi sau da kafa da saka tsari kan albarkatun kasa na man fetur da iskar gas, ta yadda za a samu janyo masu zuba jari cikin kasa,
Yan kasar ta Nijar dai sun jima suna tambayar kansu irin kudadan da kasar ke samu. Tun bayar shigarta cikin sahun kasashe masu mai da iskar gas, da kuma batun zinariya da ake hakowa a kasar ta Nijar.