Nijar: MDD ta dakatar da aiki a yammacin kasar
May 9, 2019Majalisar Dinkin Duniyar ta dauki wanann mataki ne bayan da a ranar Talatar da ta gabata wasu 'yan bindiga saman babura suka kai farmaki a sansanin 'yan gudun hijirarta da ke a garin Tabarey Barey inda suka yi awon gaba da motoci biyu na kungiyoyin agaji da ke aiki a sansanin.
Tuni dai Majalisar Dinkin Duniyar ta bai wa ma'aikatanta a yankin izinin dakatar da aikinsu, lamarin da ka iya kara jefa al'ummar yankin wacce ke dogaro da ayyukan jin kan Majalisar Dinkin Duniyar domin rayuwa a cikin halin ni 'yasu.
Dubunnan 'yan gudun hijirar kasar Mali ne dai ke rayuwa a sansanin garin na Tabarey Barey wanda ya sha fuskantar hare-hare daga 'yan bindiga da ke fitowa daga kasar ta Mali. 'Yan gudun hijirar kasar Mali sama da dubu 55 ne ke samun mafaka a kasar ta Nijar tun a shekara ta 2012 musamman a yankunan jihohin Tillabery da Tahoua da kuma birnin Yamai.