Nijar: Matakan kare kai daga sanyin hunturu
December 24, 2019A Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen Kudu da Sahara, yanayin sanyin hunturu na fara wa ne a karshen shekara musamman a watan Disemba. Kuma a mafiyawancin lokutta yanayin sanyin na zuwa ne tare da yanayin kura da ke turnuke yankunan da dama na kasar ta Nijar. Jihar Damagaram na daga cikin jihohin da yanzu haka suka tsinci kansu a cikin wannan yanayi na sanyin hunturun da kuma kura. A kan haka ne likotoci a yankin suka dukufa wajen gargadin jama'a kan su gaggauta daukar matakan kare kansu daga kamuwa da cututtuka irin su mura da toshewar nunfashi da ma takurewar fata da dai sauran cututtukan da ke da nasaba da sanyin da kuma kura a irin wannan lokaci.
Kuma ba bisa dukkan alamu, gargadin da likitocin ke yi kusan a kowace shekara tun kafin zuwan sanyin wasu magidanta suke daukar matakai da wuri na sayar wa iyali kayan sanyi musamman kananan yara da magungunan mura da sanya labule mai kauri a kofofi da tagogi da kuma dumama dakuna. Likitoci na kuma gargadin iyaye mata da su daina yi wa yara wanka a kai-a kai, da kuma shafemasu jikunsu da mai a lokuttan kwanci ko na tafiya makaranta.
A yanzu haka dai a birnin na Damagaram tun misalin 11 na dare zirga-zirgar jama’a ta rage a kan hanyoyi hatta da wuraren shakatawa jama’a sun saka manyan rigunan sanyi, a ya yinda wasu kuma suka soma hasa wuta a bakin titi inda jama'a ke taruwa suna jin wutar da kuma rage dare.