Nijar: Kungiyoyin mata sun yi Allah wadai da harin Inates
December 19, 2019Wannan taron gamgami dai na hadin gwiwar kungiyoyin matan na Nijar na zuwa ne kwanaki tara bayan harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Nijar sama da 70 da ‘yan ta’adda suka hallaka a barakin sojoji na Inates da ke a yammacin kasar kan iyaka da Mali, kuma kwana daya bayan da ‘yan kasar ta Nijar suka yi shagulgullan cikon shekaru 61 da Nijar din ta zama Jamhuriya. Sai dai mutuwar sojojin na Nijar sama da 70 na barakin sojoji na Inates da ke iyaka da kasar Mali, ya kara haifar da ce-cekuce a tsakanin masu fafutukar ganin an kori sojojin kasashen waje daga kasar ta Nijar musamman ma sojojin Faransa da ta yi wa kasar ta Nijar mulkin mallaka. A wata sanarwa da suka bayar a ranar 17 ga wannan wata, jam’iyyun da ke goyon bayan gwamnatin ta Nijar sun yi Allah wadai da wadanda ke neman ganin an kori sojojin na kasashen waje daga Nijar inda suka ce tamkar suna goyon bayan ‘yan ta’addar ne.