An kafa kungiyar mawaka ta Sogha a shekara ta 2005 a lokacin da Nijar ke shirin karbar wasannin kasashe masu amfani da harshen Faransanci na Francophonie, inda aka dauko wasu mata mawaka da suka shahara a fagen waka a Nijar daga kungiyoyi dabam-dabam kana aka hade su a karkashin kungiya daya da aka yi wa suna Sogha wacce aka dora wa nauyin tsara wakar tabben baki da za su halarci wannan biki.
To amma bayan kammala bikin shahararrun matan mawaka sun ci gaba da zama a tare a karkashin wannan kungiya ta Sogha inda suke tsara wakoki na nishadantarwa da fadakarwa da kuma raya al'adun Nijar. Sai dai batun kare hakkin mata da yara musamman a fannin ilimi ya kasance a sahun gaban maudu'an da suka fi mayar da hankali kansu a cikin wakokin nasu. Sai a saurari shirin domin jin cikakken bayani.