Nijar: An nemi gwamnati ta sako masu fafutuka
June 15, 2020Talla
A dazu- dazun nan ne gamayyar kungiyoyin fararan hulla masu fafutikar kare hakkin jama’a na Jamhuriyar Nijar, suka fitar da wata sanarwa inda suka tunatar da al’umma cewa abokansu ’yan kungiyoyin fararan hulan nan da aka kama, a wannan Litinin sun cika watanni uku ba tare da an same su da laifin komai ba.
Gamayyar Kungiyoyin sun nemi a sakesu, bayan da suka yi Allah wadai da kamun da aka yi wa ‘yar jaridar nan Samira Sabou da ita ma ake tsare da ita bisa korafin da dan shugaban kasar ya shigar, na cewa Samira ta yi mishi kage. An kasa kunne don jin martanin da gwamnati za ta mayar bayan wanann koken na wannan Litinin.