Yaushe gwamnatin Nijar za ta saki Bazoum?
July 22, 2025Kungiyar matasan ta kuma sanar da aje takardar neman izinin gudanar da zanga-zangar lumana a cikin kasar a ranar Lahadi 27 ga watan Yulin 2025 da muke ciki a kan bukatar sakin zababben shugaban kasar da sojojin suka kifar da gwamnatinsa da ma sauran matsaloli da suka dabaibaye Jamhuriyar ta Nijar. Wannan na zuwa ne, a daidai loakcin da ya rage kwanaki kalilan a cika shekaru biyu da juyin mulkin da ya yi awon gaba da gwamnatin ta tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum. A cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar matasa mai suna Mouvement Independant Pour un Niger Nouveau Dans la Justice et l'Egalite (MINNJE) a takaice, ta yi wanann kira ga gwamnatin ta gaggauta sakin hambararren shugaban kasar.
Kwanaki hudu kacal ne suka rage, a cika shekaru biyu da sojoji a karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani suka kifar da gwamnatin tasa. Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yulin 2023, wata kungiya ta cikin gida ta bukaci gwamnatin mulkin sojan da ta sallami hambararren shugaban kasar da ake rike da shi a gidan jagoran mulkin sojan. Sai dai ba dukkan 'yan Nijar ne ke goyon bayan sakin hambararren shugaban kasar ba, Hajiya Housseina Maizoubou wata 'yar fafutuka da ke goyon bayan gwamnatin Tchiani na daga cikin masu adawa da batun sakin nasa. Sai dai ta ce, akwai bukatar yin adalci a fannin shari'a a kasar.
Yanzu dai al'ummar kasar sun kasa kunne suna sauraran amsar da ma'aikatar magajin gari za ta bayar a game da bukatar neman izinin gudanar da zanga-zangar lumanar da matasan suka yi, a yayin da a hannu guda gwamnatin mulkin sojan ta sanar da soke illahirin shagulgulan raya ranar zagayowar shekaru biyu da juyin mulkin da maye gurbinsa da saukar al-Kur'ani mai girma da addu'o'i a fadin kasar domin kare ta daga abin da gwamnatin ta kira sharrin makiya da kuma fatan Allah ya sabko da damina mai albarka a kasar.