Nijar: Kashedi ga malamai kan sukar juna
March 25, 2025Gwamnatin ta yi wannan kashedi ne a wani babban taron da ma'aikatar cikin gida da ofishin gwamnan Yamai suka gudanar wanda ya hada malaman addinai na kasar inda suka yi masu hannunka mai sanda a game da kalaman kyama da wariya da suke furtawa a cikin wa'azinsu, kalaman da gwamnatin ta ce na iya tayar da fitina a cikin kasa.
Jamhuriyar Nijar dai kasa ce da ke ikirarin cewa kaso 99 cikin dari na al'ummarta Musulmai ne Kiristoci da mabiya sauran addinai, bori da maguzanci na rike da kaso daya cikin dari. A Nijar dai mabiya mabanbanta addinan na zaune lami lafiya shekaru da dama. To sai dai a shekarun baya bayan nan wannan kyakkyawar dangantakar da aka sani a tsakanin al'ummomi na neman lalacewa musamman tun bayan nada wata Farfesa Kirista a matsayin Ministar Ilimi ta kasa a gwamnati.
A yayin da a share daya, shugaban kasar Janar Abdourahmnae Tchiani ya karbi bakuncin tawagar shugabannin bokaye da 'yan Bori na kasar a fadarsa. Tun daga wancan lokaci ne wasu malaman Islama suka shiga caccaka da sukar lamirin gwamnatin musammana a shafukan sada zumunta suna zarginta da cin amanar 'yan Nijar. To a cikin wannan yanayi ne ma'aikatar cikin gida ta kasar da ma gwamnan Jihar Yamai suka kira malaman addinan da masu unguwani inda suka yi kashedi ga malaman kamar dai yadda Birgediya Janar Assoumane Harouna gwamnan birnin na Yamai ya bayyana.
Gwamnatin Nijar ta sha alwashin hukunta duk wata kungiya ko Malami da aka samu yana irin wannan wa'azi na kyamar mabiya sauran addinai a cewar Malam Ayouba Abdourahmane shi ne Magatakardan ma'aikatar cikin gida.
To sai dai shugaban babbar kungiyar addinin Muslunci ta kasa AIN Cheick Djibrilla Karanta ya ce akwai bukatar gwamnatin ta bai wa majalisar malaman addinin Islama ta kasar cikakken iko na kula da batun wa'azi idan ana son a samar da tsari na kauce wa irin wannan matsala.
Sai dai wasu 'yan Nijar na ganin matsalar da ya kamata gwamnatin ta mayar da hankali wajen magancewa ita ce yadda sannu a hankali rikici tsakanin bangarorin musulmi masu banbancin akida tsakanin 'yan darika da 'yan Izala da kuma 'yan Shi'a a makobciyar kasa Najeriya ke yin tasiri a Nijar da ma yin barazana ga makomar zaman lafiyar al'ummar kasar.