An haramta 'yan farar hula su yi zanga-zanga a Nijar
October 9, 2020Talla
Tun da farko dai hukumomin birnin Niamey sun yi fatali da yunkurin kungiyoyin ne saboda abinda suka kira kasa cika wasu ka'idodin na shari'a a gabanin sahalemasu shirya zanga-zangar ta lumana.
Sai dai tuni jagororin zanga-zangar suka bayyana anniyarsu ta zuwa gaban kotu in ji Moussa Tchangari na hadin gwiwar kungiyoyin Alternative. A farkon wannan watan ne dai wata kotu ta sallami wasu jiga-jigan kungiyoyin farar hula uku da gwamnatin kasar ta kama tsawon watanni shida bisa shirya zanga-zanga a kasar ba tare da ka'ida ba.