Nijar: Gwaji na bincike wa jama'a a kan cutar sankara
February 4, 2025A shekarar bana hukumar yaki da cutar sankara a Nijar ta mayar da hankali ne ga yin gwajin binciken cutar ga jama’a da kuma musamman fadakar da su kan matakan rigakafin hana kamuwa da ita.
Mme Habou Rahamou Abdou mai kula da harkokin sadarwa a babban cibiyar yaki da Cutar sankara ta kasa ta bayyana muhimmancin wanann shiri na wayar da kai a game da wannan cuta:
''Muna so mutane su gane cewa shi ciwo ba ma wai na sankara ba kadai, duk ciwo da ka ji shi ka zabura ka zo likita.
In ka zo likitacikin ikon Allah ana samu a ciwo kanshi. Kamar yanzu mu nan a Nijar akwai wasu abinci da ake shigo mana da su daga kasashen waje cikin gwangwani ana sa sinadarai cikinshi ana rufewa.
Sai ya yi shekaru da dama da kuma wani su maggi duk wadannan suna taimaka wa wajen haddasa cutar Sankara. Shi ya sa muke bayar da shawara kan jama'a su mayar da hankali ga cin abincinmu na gargajiya.
Malama Aichatou Madougou na daga cikin matan da suka halarci wannan taron gangami na wayar da kai ta kuma yi mana karin bayani a game da muhimmancin daukar matakan rigakafin kamuwa da cutar ta sankara :
'' Kanwata na fama da matsalar sankarar nono. Dan kululu da ake ji ga nono shi aka fidda mata. Amma kuma ba a yi shekara biyu ba sai ga shi ya sake dawowa.
Shi ya sa daga likitar Damagaram aka turo mu na ta Yamai. Kenan da dai an kula da haka ba ta faru ba. Domin yanzu muna cikin tashin hankali, ga kashin kudi har ba iyaka ga kuma ciwo.''
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa ta ce Jinkirin da jama'a ke yi wajen zuwa likita da tsadar kudin mangugunan sankara ko na yin tiyatarta da kuma rashin wadatattun kaya aiki a gidajen asibiti na daga cikin dalilan da suke sa cutar sankara na yawon kashe mutane a kasar.
Alkalumman ma'aikatar kiwon lafiya dai sun nunar da cewa cuar sankara na karuwa ne a kowace shekara a Nijar kuma mata ne suka fi fama da wannan larura musamman ta nono kuma su ne suka fi mutuwa a sakamakon kamuwa da cutar.