Nijar: Muhawara a kan dokar haramta fitar da dabbobi
May 12, 2025A yayin da masu sana' ar dabbobin ke kallon matakin a matsayin wata takurawa, wasun kuwa na ganin matakin zai yi matukar tasiri wajen sasauta farashin dabbobin musamman a daidai wannan lokacin na gabanin sallar layya.
Jahar Tahoua dai na zaman sahun gaba daga cikin yankunan kasar inda kiyo ke zaman kashi bayan tattalin arzikin kasar.
To sai dai kuma sannu a hankali sana'ar dabbobin da a can baya ke tsakanin 'yan Nijar ta koma tsakanin al'ummomin kasashen waje irin su Aljeriya da Côte d' Ivoire da Ghana da kuma Najeriya da sauransu. To dama dai wasu daga cikin 'yan kasar sun fara danganta tsadar farashin dabbobin da fitarwa da suke yi waje.
Wannan né ya kai gwamnatin daukar matakin haranta fitar da dabbobi ya zuwa ketare. Sai dai tuni a Tahoua kungiyar masu sana'ar dabbobin suka gudanar da wani zaman taron watsi da dokar kamar yadda shugaban kasuwar dabbobin Malam Rabiou Issa ya bayyana.
To sai dai kuma a dai share daya, wasu daga cikin 'yan kasar na ganin wannan matakin ba bakon abu ba ne a kasar.Matakin dai ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin al' umma, ga malam Bubakar Bakala Sule ba ko wace doka ce ba ake iya kallo a matsayin ingantatta ga al'umma.
To a yayin da wasu ke watsi da dokar wasu na ganin gwamnatin ita ma rago wasu sharudda ga dokar duba da yadda satar dabbobi daga 'yan ta'adda, da ambaliyar ruwa da ma wasu cututtuka suka batar da dubban dabbobi a kasar. To ala kulli halin dai duk yadda farashi ya sauka ko shakka babu za a samu a daya bangaren wadanda za su yi cizon yatsa sakamakon rashin kudin da suke fama da shi.