Nijar za a fara sauraron hirarrakin jama'a na tarho
June 1, 2020Dukkanin ‘yan majalisar dokokin kasar ta Nijar ne na bangaran masu rinjaye suka amince da wannan doka da za ta bai wa gwamnati damar sauraron hirarrakin jama’a ta yanar gizo da dai sauransu, a wani mataki na neman dakile wasu miyagun ayyuka. Sai dai tuni ‘yan majalisar na bangaran adawa suka nesanta kansu da wannan doka da suke ce ba komai ba ne illa kawai cin amanar ‘yan kasa ta hanyar sauraron sirrinsu wanda shi ne abin da ya rage musu daga cikin damar da doka ta ba su a cikin tsari na Dimukuradiyya. Da yake magana kan batu dan majalisar dokoki Alhaji Idrissa Maidaji na bangaran masu rinjaye, cewa ya yi wannan mataki da suka dauka na amincewa da wannan doka, babban ci gaba ne ga kasar ta Nijar, saboda ya ce wata babbar dama ce su ‘yan majalisar dokoki suka bai wa gwamnati domin dakile ta'addanci.
Yaki da ta'addanci ko leken asiri na masu adawa da gwamnatin ta Nijar
'Yan adawar na kallon kudirin dokar a matsayin wani sabon yunkuri na ganin gwamnatin ta taka birki ga wanda ta ke so. Shugaban jam'iyyar MPN kishin kasa daya daga cikin jam'iyyun siyasa na adawa Ibrahim Yacoubou. Ya ce abin da ya kamata gwamnatin ta mayar da hankali a kai shi ne kaddamar da bincike a game da sama da fadin da aka yi a game da batun cinikin makamai, a maimakon yin amfani da batun ta'addanci wajen rufe bakin 'yan adawar.