Najeriya: Wanne hali al'ummar Mokwa ke ciki?
June 4, 2025Rahotanni sun nunar da cewa fiye da mutane 200 suka halaka a wannan ibtila'i, yayin da wadanda suka tsira da rayukansu ke cikin halin tagayyara da neman dauki. Jinkirin kai musu dauki ya sanya kungiyoyi masu zaman kansu, suka fara daga murya. Kungiyar gamaiyyar yankin arewacin Najeriya masu rajin bunkasa dimukuradiyya sun bayyana bukatar gwamnati ta sa a bude baitil mali, domin tallafawa mutanen da abin ya shafa.
Hankula dai sun tashi a tsakanin mutanen da abin ya shafa kan tsarin tallafa musu, inda suka bayyana rashin jin dadinsu tare da fatan tallafin ya shiga hannunsu. Akwai shugabanin al'umma da suka bi sahu na neman kai dauki na gaggawa, ga al'ummar unguwar Hausawa ta garin na Mokwa. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA, ita ce aka fi sanya ido a kanta da matakin jihar Niger da ma karamar hukumar Mokwa.
Bayanai na nuna cewa kungiyoyin kasa da kasa Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da suka kai agaji, sun fara isa garin na Mokwa yayin da kungiyar Tarayyar Turai EU ke nata shirin na kai dauki ga wannan al'umma da take cikin nawuyacin hali na bukatar abinci da muhalli, domin dan abin da suka tanada duka ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da shi.