Nguema ya dauko hanyar lashe zaben shugaban kasar Gabon
April 13, 2025Shugaban gwamnatin sojin Gabon da ya rikide zuwa ‘dan dimokiradiyya bayan juyin mulki a 2023, Brice Oligui Nguema, ya dauko hanyar lashe zaben shugaban kasar.
An dai rufe rumfunan zabe a jiya Asabar 12 ga watan Afrilun 2025, da ake hasashen cewa Nguema zai lashe zaben wanda kuma ‘yan adawa ke zargin an tafka magudi, domin sharewa shugaban hanyar kasancewa a kan karagar mulki.
Karin bayani:Gwamnatin mulkin sojan Gabon ta nada majalisa
Babban abin da sojojin suka yi yakin neman zabe da shi ya hada da batun yaki da cin hanci da rashawa da kuma shafe tasirin iyalan Omar Bongo Ondimba da ‘dan sa Ali Bongo da suka shafe shekaru sama da 50 suna sharafinsu a mulkin kasar ta Gabon.
Karin bayani:Raba gardama: An haramtawa zuri'ar Bongo tsayawa takara
Ma'aikatar Cikin Gida ta Gabon ta fitar da sanarwar cewa mutane 920,000 suka cancanci kada kuri'a, wanda kuma ake hasashen kashi 87.12% bisa 100 sun kada kuri'a.