Netanyahu ya ce Isra'ila za ta mallake Gaza
May 22, 2025Yayin da manyan kawayen Isra'ila ke cigaba da nuna mata yatsa kan jefa rayuwar fararen hula cikin hatsari saboda hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jaddada aniyar karbe iko da dukkannin yankin a karshen farmakin da dakarunsa suka fara.
Netanyahu yace "Dukkanin zirin Gaza zai kasance karkashin ikon tsaron Isra'ila, kuma za a fatattaki Hamas gaba daya. Domin mu ci gaba da 'yancin gudanar da ayyukanmu, da kuma ba da damar manyan abokanmu su ci gaba da ba mu goyon baya, amma dai dole mu kiyaye tagayyarar al'umma mafi muni yayin cimma wannan manufa."
Abubwan da suka dauki hankali a yankin Gabas ta Tsakiya
Netanyahu ya fadi haka ne sa'o'i bayan da sojojin Isra'ila suka bude wuta da sunan gargadi a kusa da wata tawagar jami'an diflomasiyyar kasashen waje da suka kai ziyara a gabar yammacin kogin Jordan, lamarin da ya haddasa sabon rikicin diflomasiya.
Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders ta ce adadin taimakon da Isra'ila ta fara bayarwa a zirin Gaza da ke fama da yaki bai wadatar ba, kungiyar ta kwatanta matakin da rufa rufa da zai nuna alamun an kawo karshen yakin.