Najeriya: Neman masu zuba jari ko gantali?
August 28, 2025Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya koma kasarsa daga wata tafiyar da ta kai shi zuwa kasashen Japan da Brazil. Bulaguro na takwas cikin watanni takwas na shekarar bana, kuma duk a cikin neman masu zuba jari da kokarin habbaka ta tattalin arziki. Tafiye-tafiyen kuma da ya zuwa yanzu, ke jawo dagun hakarkari tsakanin 'yan kasar da ke ganin hakan a matsayin Tinubun ya karkatar da hankalinsa zuwa kasashen waje.
Karin Bayani: Sabanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa
Ya zuwa watan Mayun wannan shekara dai, fadar gwamnatin Najeriyar ta ce shugaban ya yi nasarar samo jarin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 50 a wani abun da ke zaman irinsa mafi girma da kuma alamun imani a kasar. Abdul Aziz Abdul Aziz da ke zaman kakakin shugaban kasar dai ya ce, Shugaba Tinubun ya dar ma sa'a a kokarin burge abokai da ma kawayen Najeriyar.
Koma ya zuwa ina Abujar take fadi ta kai a kokarin sauyin lamura, har ya zuwa yanzun babu abun nunawa cikin batu na yawon na Shugaba Tinubu a fadar Bello Maigari da ke zaman jigo a jam'iyyar ADC ta adawa.Shekara da shekaru dai rashin wuta da ma matsalar tsaro ne, ake alkanta rashin masu zuba jarin na kasashe na waje da su.
Karin Bayani: Hulda tsakanin Najeria da Jamus ta karfafa
Har ya zuwa yanzu dai, a fadar Farfesa Muttaqa Muhammad Usman da ke zaman kwararre a fannin tattalin arziki babu alamun sauyi a jerin matsalolin. Kokarin neman masu zuba jari ko kuma barna da dukiyar 'yan kasa, ya zuwa watan Yunin shekarar ta 2025 da muke ciki dai Abujar ta batar da abun da ya kai Naira miliyan dubu 23 da sunan yawo na shugaban kasar zuwa kasashe na waje.