Neman dinke baraka a jam'iyyar CDS a Nijar
June 10, 2013A Jamhuriyar Nijar mataimakin shugaban jam'iyyar CDS Rahama Alhaji Abdou Labo ya yi tayin sasantawa da abokanin hamayyarsa na bangaren Alhaji Mahaman Usmane shugaban jam'iyyar na kasa baki daya. Wannan domin hada kan 'ya'yan jam'iyyar da nufin farfado da martabarta da matsayinta a fagen siyasar kasar kafin zuwa zabuka masu zuwa. Sai dai kuma ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da zama a cikin gwamnati, inda yake rike da mukamun ministan harkokin cikin gida.
Mataimakin shugaban jam'iyyar ta CDS Rahama wanda shine shugaban jam'iyyar reshen Jihar Maradi ya yi wanann tayi ne lokacin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yamai.
Alhaji Abdou Labo ya yi godiya wa 'ya'yan jam'iyyar da suka tsaya masa duk tsawon lokaci da aka shafe ana shari'a har zuwa lokacin da kotu da ba shi gaskiya. Kuma ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya kira, wanda shi ne karo na farko da ya yi wani tsokaci tun bayan hukuncin kotun kolin kasar a makon da ya gabata. Rikicin da ya hada shi da bangaren shugaban jam'iyyar ta kasa baki daya Alhaji Mahaman Usmane. Wani babban taron congres da jamiyyar ta shirya ne a shekara ta 2011, ya dauki matakin tsige Abdou Labo da wasu makarabansa daga cikin jam'iyyar, kafin kotun kolin kasar ta karya wanann mataki dama duk wasu matakan da taron congres din ya dauka a baya.
Duk da irin cece-kucen da aka kwashe watanni 28 ana yi tsakanin yayan jam'iyyar lokacin taron manema labaran da ya kira Alhaji Abdou Labo ya nemi runguman juna, domin tabbatar kawo karshen barakar da ke cikin jam'iyyar.
Amma ganin cewa a yau kotu ta sake tabbatar da kasancewar Abdou Labo da makarabansa a matsayin 'ya'yan jam'iyyar ta CDS Rahama ko zai amince ya yi murabus daga mukaminsa na minista da ya ke rike da shi a yau ganin cewa dokokin kasar Nijar sun haramta wa dan adawa shiga gwamnati. Sai ya amsa da cewa ko kadan ba haka zancen yake ba. Kuma zai ci gaba da zama daram bisa mukamun.
Yanzu haka dai wasu 'ya'yan jam'iyyar ta CDS Rahama na zargin Abdou Labo da makarabansa da kasancewa wasu soji haya na wasu jam'iyyun da ke mulki, domin rusa jam'iyyar ta CDS RAHAMA baki daya. Zargin da ya yi watsi da shi..
Yanzu da ake ganin ba abin da ya rage wa jam'iyyar ta CDS Rahama illa komawa shirya sabon babban taro na kasa, lauyan jam'iyyar ya bada sanawarwar daukaka kara a kotun Kungiyar Habaka Tattalin arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (CEDEAO). Da yake mayar da martani Abdou Labo ya ce a shirye suke domin kare matsayinsu a gaban ko wace irin kotu.
'Yan kasar ta Jamhuriyar Nijar na ci gaba da zuba ido, domin ganin yadda abubuwa za su kasance cikin jam'iyyar wadda a baya ta rike madafun ikon kasar.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Suleiman Babayo / MNA