NATO ta amince da kara kudade ga fannin tsaro
June 26, 2025Talla
Shugabannin sun jaddada cikakken goyon bayansu ga kudurin tsaron hadin gwiwa na NATO, wanda ke tabbatar da kariya ga duk membobin kungiyar kawancen tsaron ta kasashen yammacin duniya, muddin dai aka kai musu hari.
Wannan sabon burin na kudin na tsaro zai maye gurbin tsohuwar manufa ta kashi 2 cikin 100, kuma ana sa ran za a cimma shi nan da shekara ta 2035.
Wannan mataki ya biyo bayan bukatar da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, wanda ya bayyana wannan yarjejeniya a matsayin babban nasara ga Amurka.
Bugu da kari, an bayyana Rasha a matsayin babbar barazana ta dogon lokaci ga tsaron yankunan Turai da Amurka, tare da yin alkawarin ci gaba da tallafa wa Ukraine a rikicin da ke tsakaninta da Rasha.