NATO na kara karfi don dakile barazanar Rasha - Merz
June 24, 2025Shugaban gwamnatin Jamus Fiederich Merz ya bayyana taron kolin kungiyar tsaro ta NATO da za bude a wannan Talata a birnin Hage na kasdar Netherland a matsayin mai cike da tarihi, tare da ba da tabbacin cewa membobin kungiyar za su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsarodon dakile barazanar Rasha, ba wai kawai don farantawa shugaban Amurka Donald Trump ba.
Karin bayani: Shin Turai ta shirya kare kanta ba Amurka?
Kafin ya tashi daga birnin Berlin zuwa birnin Hage domin halatar taron koli na NATO, Merz ya yi jawabi a gaban majalisar dokoki ta Bundestag inda yake ce: ''Muna yin haka ne ba don mu farantawa Amurka ba kamar yadda wadansu ke tunani. Muna aiki ne bisa radin kanmu domin Rasha ta zama babbar barazana ga tsaro da kuma 'yancin daukacin kasashen nahiyar Turai.''
Jamus dai na ci gaba da aiki tukuru domin kara inganta taronta, tare da burin kai wa ga saka kashi 3,5 na karfin tattalin arzikinta a wannan fanni kafin shekarar 2029, abinda kuma zai zarta matakin da kungiyar NATO ta bukaci membobinta suka kai kafin wannan lokaci.