Nandi-Ndaitwah ta zama shugabar Namibiya ta farko
March 21, 2025An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin sabuwar shugabar kasar Namibiya a ranar Juma'a bayan lashe zabe da ta yi watanni uku da suka gabata.
Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar ta kasance mace ta farko da ta shugabanci Namibiya da ke kudancin Afirka.
Kotun Namibia ta kori karar 'yan adawa da ke neman soke zabe
Itace kuma mace ta hudu da ta taba rike mukamin shugaban kasa a nahiyar bayan Ellen Johnson-Sirleaf ta Laberiya da Joyce Banda ta Malawi da kuma Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya.
An zabi 'yar shekara 72 din ce a shekarar da ta gabata inda ta samu nasara da kashi 58.1% na kuri'u da aka kada.
Adawa da yarjejeniyar kisan kiyashi da Jamus ta aikata a Namibiya
Nandi-Ndaitwah ta ce za ta mayar da hankali ne kan yaki da rashin aiki da matasan Namibia ke fama da shi sannan za ta inganta harkar noma da samar da ababen more rayuwa a wa'adinta na shekara biyar.