Namibiya na bikin shekaru 100 da kisan gillar mutanensu
May 28, 2025Talla
Kasar Namibiya na gudanar da bikin cika shekaru 100 na tunawa da kisan gilla da Jamusawa suka yi wa 'yan kasar kusan 70,000, gwamnatin Windhoek na danganta matakin a matsayin kisan kiyashi na farko a karni na 20.
Namibiya: Diyya muke bukata ba tallafi ba
A shekarar 2021 gwamnatin Jamus ta dauki alhakin kisan dubban mutane a zamanin mulkin mallaka a kasar Namibiya tare da neman afuwar 'yan kasar kan abin da ya faru a wancan zamani.
Jamus ta yi alkawarin bai wa gwamnatin Namibiya tallafin kudi sama da yuro biliyan daya, wanda zai taimaka wajen gina kasar daga lokacin har tsawon shekaru 30, sai dai matakin bai samu karbuwa ba daga cikin Namibiya.