You need to enable JavaScript to run this app.
Tsallake zuwa shafin jadawali
Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bidiyo
Shirye-shiryen DW Hausa
Yankuna
Najeriya
Nijar
Afirka ta Yamma
Sassa
Siyasa
Zamantakewa
Wasanni
Mayar da hankali
Ilimin Fasahar Zamani
Shirye-shiryen DW Hausa
Bidiyo
Talabijin kai tsaye
Talla
Najeriya
Najeriya kasa ce da ke yammacin Afirka kuma ta na kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Tsallake zuwa bangare na gaba Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji za a ji yadda hukumar 'yan sandan Najeriya ta musanta jifa da ihun da aka yi wa tawaga Shugaba Buhari a Katsina, dan takarar jam'iyyar NNPP Kwankwaso ya goyi bayan masu kalubalantar bakin CBN kan wa'adin karbar kudin Naira.
Fina-finan da za su yi zarra a 2023
Bayan faduwar kasuwannin CD da DvD, masu fina-finan Hausa sun koma YouTube don nuna shirye-shiryensu masu dogon zango.
Rudani jama'a na kin karbar tsohuwar Naira
An shiga rudani a Najeriya kan rashin sabbin kudi yayin da wa'adin karbar tsofaffin ke karewa
Najeriya: Martani kan kisan Fulani makiyaya
Jirgin sama ne ya jefa wa makiyayan masu bama bamai a wani irin yanayi mai daure kai da ya bar ayar tambaya.
Makiyaya 27 sun mutu a harin bam
Kungiyar fulani ta zargi jirgin sojojin Najeriya ta sake bama-bamai da ya kashe mutane 27 da shanu masu yawa a Nasarawa.
Shirin Yamma
Faransa ta bayyana cewa ta samu sakon daga sojojin da ke mulkin kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka, domin neman janye dakarun kasar ta Faransa a kasar da ke yankin Sahel.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, Babban Bankin kasar CBN ya karyata cece-kucen da ake yi kan kudin da aka tara a matsayin harajin hatimin kan sarki. A Jamhuriyar Nijar kuwa, gamayyar kungiyoyin kwadago na ITN sun fara yajin aiki.
Makomar 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi
Murna ta koma ciki ga burin kananan hukumomin Najeriya na samun 'yancin cin gashin kai
Najeriya: Sana'ar sarrafa mazarkwaila
Nazari kan sabuwar fasahar da masu sarrafa rake ya koma mazarkwaila ke amfani da ita a Kaduna
Taba Ka Lashe 17.01.2023
Yadda al'adar Fulani ta auren gida ta fara sauyawa sannu a hanakli a Najeriya.
Gudun auren mata masu kaki a Najeriya
Fargabar abin da ka je ya zo, na sanya tsoron tunkarar matan da ke sanya kaki da kayan sarki a Najeriya.
Dubban mutane sun bace a Najeriya
Rikicin Boko Haram da ya kwashe sama da shekaru 13 a Najeriya, ya yi sandiyyar raba miliyoyin mutane da gidajensu.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa, alkalumma kungiyar agaji ta ICRC sun yi nuni da cewa, kimanin mutane dubu 26 ne suka bace sakamakon rikicin yankin arewa maso gabashin Najeriya. A Nijar, kungiyoyin fararen hula sun yi kira kauracewa kasuwanni sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin ilimi. Za kuma a ji yadda karatun 'ya'ya mata a jamhuriyar Nijar ke fuskantar kalubale.
Shirin sake gina Tafkin Chadi
Wakilai na yankin Tafkin Chadi da na kasashen Jamus da Norway sun hadu a Nijar don nazarin hanyoyin sake gina yankin da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji a kasar Burkina Faso garkuwa da mutane da yan bindiga ke yi na daukar wani salo da ke neman haddasa rudani a yammacin Afirka.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji shirye-shirye kamar ku shiga Kulob da Abu Namu da shirin Zabi Sonka da Wasikun Masu Sauraro
Shirin Rana
A cikin shirin za aji shirin Ku Shiga Kulob da Amsoshin Takardunku da Ciniki da Masana'antu da Wasikun masu Sauraro
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji shirin Afirka a Mako da bitar wasu muhimman batutuwan da suka ja hankali a Afirka bayan an ji labaran duniya
EU na fargaba kan makomar zaben Najeriya
Manyan kasashen yammaci na Turai sun gargadi 'ya'yansu da su kaucewa ziyartar Najeriya.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa Nijar ana cece-kuce kan karin shekarun tafiya ritaya, a Najeriya masarautar Katsina ta tube wani hakimi bisa zargin hadin baki da 'yan bindiga.
Gaskiyar Magana: Kalubalen samun kudin kamfen ga mata da matasan da ke takara
A wannan makon shirin ya duba kalubalen samun kudaden yakin neman zabe ga mata da matasan da ke takara a zaben Najeriya. Mun gayyato muku Hajiya Laila Buhari, mai takarar sanata a shiyyar Kano ta Tsakiya a jam'iyyar PDP da kuma Jamilu Adullahi Ajiwa, wani matashi da ke takarar majalisar jiha a jam'iyyar PRP ta jihar Katsina.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji cewa, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri da zai gwama karatun addini da na zamani a makarantun tsangaya. A Nijar, wata mata ta kai karar wani likita bayan da ya cire wa 'yarta mahaifa ba tare da izinin iyayenta ba. Akwai rahoton Kundin 'yan mata da ya duba matsalar fyade.
Najeriya ta fara shirin zare tallafin man fetur
Gwamnatin Najeriya ta ce ta dauki matakin fara shirin zare tallafin man fetur tun daga watan Aprilun da ke tafe.
Najeriya za ta fara shirin zare tallafin man fetur
Gwamnatin Najeriya ta ce ta dauki matakin fara shirin zare tallafin man fetur tun daga watan Aprilun da ke tafe.
Shirin Rana
Za a ji cewa an kama wasu sarakunan gargajiya a jihar Edo kan zarginsu da hannu a sace fasinjojin jirgin kasa.
Dandalin Matasa
Shirin ya duba tattaunawa kan ilimin matasa a Najeriya yayin da ake shirin zabukan kasar.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji yadda wani mahaifi a jihar Baucin Najeriya ya aurar da 'yarsa cikin wasa, matakin da malaman addini ke bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta.
Barazanar tashin hankali a zaben Najeriya 2023
ECOWAS da Majalisar Dinkin duniya sun yi gargadi a kan rigingimun siyasa gabanin gudanar da zaben Najeriya.
Shirin Rana
A Jamhuriyar Nijar kamfanonin wayar sadarwa da suka yi karin kudin Data na Intanet da na kira sun yi amai sun lashe, inda duk suka koma a kan tsohon farashinsu.
Ko mata na da tasiri a siyasar Najeriya?
Mata fiye da miliyan tara ne suka karbi rijistar zaben 2023 a Najeriya, sai dai ana zargin maza da rashin bai wa matan dama a fagen siyasar kasar. Shin yaya tasirin shugabancin mata? Mai yasa ba sa samun goyon bayan 'yan uwansu mata? Shin da gaske mata suna da rauni a fannin shugabanci ko suna da adalci fiye da maza?
Shirin Safe
Za a ji yadda masana siyasa suka ba da shawarwari kan zaben 2023
Takaddamar kasuwar magani a Kano
Gwamnatin Kano ta bukaci 'yan kasuwar magani su gaggauta komawa sabon matsuguninsu
INEC ta jaddada gudanar da zabe a Febrairu
INEC ta ce ba za a dage zaben shugaban kasa ba duk da kalubalen tsaro.
Najeriya: Martani kan hasashen yunwa a 2023
Miliyoyin 'yan Najeriya za su fuskanci barazanar yunwa a 2023
Cin-hanci tsakanin matasan Najeriya
Ko akwai mafita kan matsalar cin-hanci da rashawa tsakanin matasan Najeriya? Ku biyo mu a wannan tattaunawar ta mu.
Matasa da rashin tsaro a Najeriya
Shin wane tanadi aka yi na tafiya da matasa a harkokin tsaro a Najeriya? Wannan na cikin batun da shirin ya tattauna.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji a Najeriya gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele ya koma bakin aikinsa bayan kwashe lokaci a kasar waje a dai-dai lokacin da ake cece-kuce a kan zargin da ake yi mishi na cin hanci da rashawa.
Shirin Safe
Shirin ya kunshi labarai da rahotanni daga sassan duniya har da halin da ake ciki a Najeriya bayan wani taron na jam'iyyar APC mai mulki.
Shirin Yamma
A cikin shirin za a ji cewa, shugabannin gwamnatocin kasashe da manyan kamfanoni na duniya suna cikin wadanda suke halartar taron tattalin arziki na duniya na shekara-shekara da aka buda a birnin Davos. 'Yan bindiga a kudancin Najeriya, sun fara sabon salon kamfe na hana gudanar da zabukan 2023 a yankin.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa aNajeriya jami'an tsaro sun bazama neman ‘yan bindigar dajin da suka kai hari a kauyen Kafin–Koro da ke karamar hukumar Paiko ta jihar Niger. A Nijar kuma yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin kasar ta kaddamar ya ritsa da wani alkali da ake zargi da karkatar da wasu kudaden gado.
Yan bindiga sun hallaka babban limamin Coci
Italiya ta yi Allah-wadai da kisan gillar da wasu 'yan bindiga suka yi wa wani babban limamin Cocin Katolika a Najeriya.
Shirin Safe
Shirin na kunshe da rahotanni da labarai daga sassan duniya.
Shin Rana
Za a ji hukumar zaben INEC a Najeriya ta tsawaita wa'adin karbar katin zabe
Najeriya: An kara wa'adin karbar katin zabe
Har yanzu akwai miliyoyin ‘yan Najeriya da ba su karbi katunan nasu ba, abin da zai iya hana su yin zabe.
Gaskiyar Magana: Fargabar tsaro a zaben Najeriya
A wannan makon shirin ya tattauna kan tsaro da fargabar da ake nunawa game da gudanar da zaben Najeriya da ke tafe. Mun gayyato muku Zainab Aminu, mai magana da yawun hukumar zaben Najeriya INEC da kuma Barrister Audu Bulama Bukarti, mai nazari harkokin tsaro a cibiyar Tony Blair da ke birnin London.
Shirin Safe
Za a ji nazari kan zargin wasu da Shugaba Buhari na Najeriya ya yi na cewar sune ke dagula harkokin tsaron kasar. A Nijar hukumomi ne ke kokarin maganta yawan haduran kan hanyoyi. A Kamaru akwai batun koma baya da ake samu a bangaren ilimi.
Shirin Yamma
A cikin shirin za a ji cewa manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na ta kokarin zawarcin kananan jam'iyyu, a wani mataki na lashe babban zaben da ke tafe, a Jamhuriyar Nijar batun karin kudin kira da na intanet, da kamfanonin sadarwa suka yi ne ke ci gaba da tada kura.
Shirin Rana.
A cikin shirin za ku ji cewa, alkaluman da hukumar zaben Najeriya ta fitar na nuni da cewar matasan kasar ke kan gaba daga cikin jerin wadanda suka yi rijistar kada kur'a a babban zaben da ke tafe. A kasar Ghana tsarin inshorar lafiyar kasar ne ke fuskantar tazgaro tun bayan kaddamar da shi shekaru aru-aru da suka gabata.
Yuwuwar hadaka a siyasar Najeriya
Yayin da suka rage 'yan makonni da babban zaben Najeriya manyan jam'iyyu na shirin hadaka da nufin kai wa zuwa gaci.
Shafin da ya wuce
Shafi 54 daga 200
Shafi na gaba