You need to enable JavaScript to run this app.
Tsallake zuwa shafin jadawali
Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bidiyo
Shirye-shiryen DW Hausa
Yankuna
Najeriya
Nijar
Afirka ta Yamma
Sassa
Siyasa
Zamantakewa
Wasanni
Mayar da hankali
Ilimin Fasahar Zamani
Shirye-shiryen DW Hausa
Bidiyo
Talabijin kai tsaye
Talla
Najeriya
Najeriya kasa ce da ke yammacin Afirka kuma ta na kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Tsallake zuwa bangare na gaba Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Batutuwan Afirka da ke jaridun Jamus
Hankalin jaridun na Jamus a wannan makon ya karkata zuwa kan babban zaben Najeriya da taron AU.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji fatan da 'yan Najeriya kan babban zaben kasar da zai gudana a gobe Asabar. A Nijar, an gudanar da taron kan batun ci-gaban jihar da abubuwan da ke hana ruwa gudu da kuma hanyoyin gyara.
Waɗanne labaran boge kuka fara cin karo da su kan zaɓen Najeriya?
Waɗanne labaran boge kuka fara cin karo da su kan zaɓen Najeriya? To ga yadda za ku tantance zare da abawa daga DW Hausa
Tasirin sauya fasalin kudi kan zaben Najeriya
Kotun koli a Najeriya ta sake dage shari'ar da take sauraro kan hana aiki da tsoffin kudaden kasar har zuwa ranar 03 ga watan Maris na 2023.Dangane da wannan, ga bidiyo kan tasirin sauya fasalin kudin ga zaben Najeriya.
Ko waye zai lashe zaben Najeriya na 2023
A wannan bidiyon, za ku ji da ganin bayanai dalla-dalla na hakikanin hasashen zaben Najeriya na 2023.
Shirin Yamma
Za a ji yadda kungiyar MASSOB ta yi watsi da barazanar IPOB na hana zabe a Kudu maso yammacin Najeriya
Najeriya: Kama makamai gabannin zabe
Fargaba a daidai lokacin da ya rage sa'o'i kalilan a kada kuri'a a zaben shugaban kasa da 'yan majalisu a Najeriya.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya kananan Jam’iyyun na ci gaba da narkewa suna komawa ga manyan Jam’iyyun da ake sa ran za su kai labari a zaben kasar, a Nijar ta'addanci na neman durkusar da aikin hakar ma'adanai a yanmacin kasar.
Dandalin Matasa: Fadikar da matasa a Najeriya saboda zabe
Shirin Dandalin Matasa ya duba yadda ake fadikar da matasa kan zaman lafiya saboda zaben da za a yi.
Tarihin 'yan takara a zaben Najeriya
Takaitaccen tarihin 'yan takara hudu da suka fi yin fice a zaben shugaban kasar Najeriya.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji yadda al'umma a Najeriya suka shiga rudani biyo bayan dage karar tsawaita amfani da tsaffin kudi a kasar.
Kotu ta sake dage shari'ar wa'adin karbar Naira
Kotu a karkashin jagorancin mai shari'a Okoro, ya saurari mahawarar da bangarori biyu suka tabka.
Shirin rana
A cigaba da kawo muku tarihin 'yan takarar shugaban kasa na manyan Jam'iyyun siyasar Najeriya a zaben da ke tafe, za a ji tarihin dan takarar Jam'iyyar Labor Peter Obi mai shekara 61 da haihuwa kuma tsohon gwamnan jihar Anambra.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji a Najeriya 'yan kwanaki kafin babban zaben kasar al'umma na ci gaba da fuskantar gagarumar matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Shirin yamma
A cikin shirin za a ji cewar yayin da ake bikin ranar harshen uwa ta duniya, albarkacin wannan rana wakilimmu a Kano Abourahman Kabir yayi mana nazari kan cigaba da harshen na hausa ya samu da kuma irin kalubalen da ya ke fuskanta
Kungiyoyi da hukumar zaben Najeriya sun gana
Hukumar zaben Najeriya da kungiyoyin saka ido kan zabe sun gana game da zaben da za a yi a karshen mako.
Taba Ka Lashe: Wasu kabilru sun hade domin fahimtar juna
Wasu kabilu kimanin takwas a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi a Najeriya sun hade wuri guda tare da dabbaka al'ada daya.
Shirin Yamma
A cikin shirin za a ji cewa, rahotanni daga kan iyakar kasashen Turkiya da kuma Siriya sun yi nuni da cewa an samu aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 6.4. Sarakunan gargajiya a Najeriya, na yin kira ga al'ummar kasar da su gudanar da zaben da ke tafe a karshen mako cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Jam'iyyar PDP ta kammala yakin neman zabe
Jam'iyyar PDP mai adawa ta kammala yakin neman zaben da za a gudanar a ranar Asabar da ke tafe.
Shirin Hausawa mazauna Legas na gudanar da zaben Najeriya.
Shirin Rana
A cikin shirin bayan Labarn Duniya, muna taafe da rahotanni da suka hadar da na bikin al'ada na Karneval da ake gudanarwa duk shekara a Jamus.
Kalubalen mata masu kananan sana'a a Najeriya
Shirin ya duba tarin kalubalen da kananan sana'o'in cikin gida da mata ke yi suka shiga tun bayan sake fasalta wasu takardun naira a Najeriya.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji yadda al'umomin kasar Kamaru ke bibiyar shirye-shiryen zaben Najeriya, sarakunan gargajiya a Nijer na kokarin farfardo da karfi da ma kimar masarautun.
Kalubalen sauya fasalin kudin Najeriya
CBN ya karyata labarin cewa ya bayar da izinin ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na Naira a Najeriya.
Shirin Yamma
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, muna tafe da rahotanni da suka hadar da na muhawara kan batun gudanar da zabuka da katin shaidar zama dan kasa maimakon rijistar zabe a Ghana. Akwai sauran rahotanni da shirye-shiryen da muka saba gabatar muku.
Gaskiyar Magana: Sauya sheka a siyasar Najeriya
A wannan makon mun duba yadda 'yan siyasa ke sauya sheka a siyasar Najeriya. Mun gayyato muku Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, daraktan tsara dabaru da kula da bayanan sirri na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a Kano. Sai kuma Barista Bello Muhammad Goronyo, sakataren jam’iyyar APC a shiyyar arewa maso yamma.
Darasin da ke tattare da rikicin kudi Naira
A kokarin Najeriya na dakatar da amfani da tsohon kudi, shirin Darasin Rayuwa ya dubi yadda matakin ke shafar magidanta.
Rikici ya jefa jam'iyyar APC cikin garari
Rikici ya barke a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kan manufofin Shugaba Muhammadu Buhari a gabanin babban zaben.
Rikici ya jefa jam'iyyar APC cikin garari
Rikici ya barke a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kan manufofin Shugaba Muhammadu Buhari a gabanin babban zaben.
Zaben Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus
Muhawara kan janye sojojin Jamus daga Mali gami da zaben Najeriya da ke tafe suna ci gaba da jan hankalin jaridun Jamus.
Shirin Safe
Bayan labaran duniya, za a ji irin shirin da matan karkara ke yi gabanin babban zaben Najeriya da ke kara gabatowa. A Nijar kuwa, kungiyoyin cikin kasar da ma na kasa da kasa ne suka shirya wani gangamin wayar da kai a kan cin zarafin bakin haure mata.
Shirin Yamma
A cikin shirin za a ji martanin 'yan Najeriya kan jawabin shugaba Buhari, a Nijar dattin leda na kasancewa babbar annoba da ke haddasa matsalar gurbacewar muhalli.
Sauya takardun Naira ya janyo kalubale
Shugaban Najeriya ya ce a ci gaba da amfani da tsohuwar takardar kudi ta Naira 200, saboda matsalolin sauyin kudin.
Najeriya: Shirye-shiryen zaben 2023
Matsaloli da suka hadar da na karancin man fetur da kuma sababbin takardun kudin Naira, na cikin kalubalen Najeriya.
Nigeria: Mata masu aikin tsaro
Einbruch in eine Männerdomäne: Ein nigerianische Security-Unternehmen beschäftigt ausschließlich Plus-Size-Frauen.
Dandalin Matasa: 16.02.2023
Shirin Dandalin Matasa ya yi nazari kan yadda 'yan siyasa ke amfani da matasa wajen yin bangar siyasa da sara suka. Shirin ya yi wannan nazarin ne ganin yadda babban zaben kasar ke kara karatowa.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa masu sharhi na martani kan jawabin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gamne da fasalin kudin Naira. Runudunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta shirya tsaf domin bayar da duk wata kariyar da ta dace wa babban zaben kasar da ke tafe kasa da kwanaki 10.
Somaliya ta shahara a batun cin-hanci
Somaliya da Sudan ta Kudu na sahun gaba, a fannin cin-hanci da karbar rashawa ko sama da fadi da dukiyar kasa a Afirka.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji cewa Shugaba Buhari na Najeriya ya yi wa 'yan kasa jawabi dangane da halin da gwamnatinsa ta samu kanta a ciki sakamakon rikicin rashin asassun kudin Naira. Gwamnati Ghana tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da shiri ne da nufin rage hadarin amfani da sinadarin Mercury.
Shirin Yamma
A cikin shirin za a ji cewar a Najeriya cibiyar ci gaban kasa da bunkasa dimukurdiyya ta Code ta gabatar da rahotonta a kan shirye-shiryen zaben kasar inda ta bayyana cewa karuwar tashe-tashen hankula da kai hare-hare da zasu iya shafar babban zaben.
Zargin sojojin Afirka da sayar wa 'yan tawaye makamai
Zargin sojojin Afirka da sayar wa 'yan tawaye makamai
Ko kudin CFA zai maye gurbin Naira?
Matakin amfani da kudin makwabciyar kasa Nijar wato CFA a Najeriya, bayan da takardar kudin Naira ta yi karanci.
Makomar hada-hadar kudi a Najeriya
Kotun kolin Najeriya ta ce, a ci gaba da karbar tsohon kudin da babban bankin kasar ya sake fasalinsu da suke wahala.
Shirin Yamma
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, za ku ji cewa har yanzu al'ummar Najeriya na kokawa dangane da halin kuncin da suka shiga sakamakon karancin takardun Naira.
Shirin Rana
A cikin shirin za a ji cewa ana mayar da martani bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da soke gudanar da zabuka a darurwan runfunan zabe a wasu jihohin kasar saboda matsalar tsaro. Hukumar ECOWAS ta yi watsi da yunkurin kasashen Burkina Faso da Guinea Conakry da kuma Mali na hadewa.
Kalubalen babban zaben Najeriya na 2023
Ba za a gudanar da zabe a rumfuna 240 da ke jihohi 28 na Tarayyar Najeriya ba in ji hukumar zaben Najeriya INEC.
Shirin Safe
A cikin shirin za a ji kiran hukumomin Agadez da ke Nijar ga matasan Najeriya na su tsaya a yi zabe da su, a Kamaru hari ya ritsa da ma'aikata biyar na Kamfanin CDC na kasar.
Shirin Yamma.
A cikin shirin za aji yadda gwamnonin Najeriya ke gargadin cewar tatalin arzikin kasar na fuskantar barazanar durkushewa sakamakon rashin kudi a hannun jama'a, a yayin da a Jamhuriyar Nijar matsalar tsaro ke neman dawowa a yankin Tillabery, hakan ta sa daruruwan makarantun boko bayana fargaba kan makomar ilimi a yankin da ma makomar matasa.
Shirin Rana
Albarkacin ranar radio ta duniya, za a ji yadda al'umma ke bayyana irin sabo da ma karuwa da suke samu ta hanyar sauraren radio.
Abu Namu: Kalubalen mata a siyasar Najeriya
A yayin da babban zaben Najeriya ke karatowa, shirin ya duba kalubale da rawar da mata suka taka daga lokacin yakin neman zabe zuwa yanzu.
Shafin da ya wuce
Shafi 52 daga 200
Shafi na gaba